Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin Dala Miliyan Biyu Daga Wuri Na, Matawalle
- Gwamnan Zamfara ya ce shugaban EFCC ya taɓa neman cin hancin makudan kudi daga wurinsa amma ya hana shi
- Matawalle ya yi wannan zargi ne a lokacin da dangantaka ke ƙara tsami tsakaninsa da EFCC
- Ya ce Bawa ya sauka daga kan kujerarsa ya ga yadda cikin yan dakiko mutane zasu fito da tulin hujjoji kan almundahanarsa
Zamfara - Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi ikirarin cewa shugaban hukumar EFCC na ƙasa, Abdulrasheed Bawa, ya nemi cin hancin dala miliyan $2m.
Daily Trust ta rahoto cewa Matawalle ya yi wannan ikirari ne a lokacin da alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, gwamna Matawalle ya buƙaci Bawa ya sauka daga kujerar shugaban EFCC domin akwai tulin tambayoyin da ya kamata ya amsa.
Amma Bawa ya maida masa martanin cewa ba bu abinda yake boye wa kuma ya roki Gwamnan ya kai ƙararsa ga mahukunta idan har yana da kwararan shaidu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wata hira da BBC Hausa, Gwamna Matawalle ya ce shugaban EFCC ba amintacce bane.
"Bai kamata ace koda yaushe sai dai a tuhumi gwamnoni ba, ba su kaɗai ke da asusun ajiya ba, gwamnatin tarayya ma tana da asusu, amma ne shugaban EFCC ya musu?."
"Kamar yadda yake bugun ƙirjin yana da shaidu a kan gwamnoni, ya fito ya faɗa wa duniya shaidun da ya tara a matakin tarayya. Shi kansa ya sauka, mutane zasu tabbatar bai da gaskiya."
Bawa ya nemi cin hanci a wuri na amma na ƙi yarda - Matawalle
Game da abinda ya haɗa shi da shugaban EFCC, Matawalle ya ci gaba da cewa:
"Na tanadi shaidu kan shugaban EFCC, ya sauka daga muƙamin ya gani, cikin 'yan daƙiƙu kalilan mutane sama da 200 zasu kawo hujjoji kan cin hancin da ya karɓa a wurinsu."
"Shi ya san abinda ke tsakanin mu, akwai abinda ya nema ban bashi ba, ya buƙaci cin hancin dala miliyan $2m daga wurina kuma ina da shaidu kan haka, ya san gidan da muka zauna, shi ya gayyace ni ya faɗa mun sharuɗɗan."
"A lokacin ya gaya mun yadda gwamnoni ke zuwa Ofishinsa amma ni bana zuwa. Idan bani da shaidar da zan dogara da ita ba zan faɗi haka duniya ta ji ba."
Ni Da Kwankwaso Muka Fara Sayar Da Gidajen Gwamnatin Kano, Ganduje Ga Abba Gida-Gida
A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje ya bayyana yadda Kwankwaso ya kawo tsarin sayar da gidajen gwamnati tun a zamanin mulkinsa a Kano.
Ganduje ya ce lokacin yana matsayin mataimakin gwamna, Kwankwaso ya sayar da kadarorin gwamnati ga ma'aikata da yan siyasa bila adadin.
Asali: Legit.ng