Kotu Ta Yanke Sabon Hukunci Kan Karar Kallubalantar INEC Da Nasarar Tinubu

Kotu Ta Yanke Sabon Hukunci Kan Karar Kallubalantar INEC Da Nasarar Tinubu

  • Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta yanke hukunci kan ƙarar da aka shigar kan Bola Tinubu da hukumar zaben ta ƙasa (INEC)
  • A ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu, kotun ta ɗage sauraren ƙarar da jam’iyyar APM ta shigar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da INEC zuwa ranar Litinin 22 ga watan Mayu
  • Jam’iyyar APM bayan nuna rashin amincewarta da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, ta garzaya kotun don ƙalubalantar nasarar Tinubu da INEC

FCT, Abuja - A ranar Alhamis 18 ga watan Mayu ne kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta ɗage ci-gaba da sauraron ƙarar da jam'iyyar APM ta shigar zuwa ranar Litinin, 22 ga watan Mayu, 2023.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, a cikin ƙarar mai lamba CA/PEPC/04/2023, jam’iyyar APM na ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotun Zabe Ta Sake Dage Sauraron Karar Atiku Abubakar Kan Nasarar Tinubu, Ta Bayyana Sabon Lokaci

Kotun ta saurari bayanan da dukkan bangarorin suka gabatar, wanda aka jera a matsayin na 1 zuwa na 4 sun haɗa da, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Kashim Shettima da Kabiru Masari.

yakubu
Kotu Ta Sake Yanke Hukunci Kan Masu Kalubalantar INEC Da Nasarar Tinubu. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Lauyan INEC, A.B Mahmoud, SAN, ya gabatar ma kotun buƙatu guda biyu da tawagarsa ta yi na neman kotu ta yi watsi da wasu sakin layi na sharhin da mai shigar da ƙara ya shigar a ranar 20 ga watan Afrilu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan sauraron bayanan da dukkan ɓangarorin suka gabatar na buƙatunsu mabanbanta, kwamitin mai mutum biyar karkashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani ya sanar da zama na gaba a ranar Litinin 22 ga watan Mayu. Daily Independent ta ruwaito.

Ƙarar Atiku kan Tinubu ta tsaya sakamakon ɗage ci-gaban shari’ar da kotu ta yi

Kara karanta wannan

Labour Da Peter Obi Sun Gaza Biyan N1.5m Don Karɓar Takardun Da Kotu Ke Nema, INEC

Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ce za ta ƙara yin zama domin sauraron ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shigar kan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kotun da ke zamanta a Abuja, ta ce za ta sake duba ƙarar da Atiku ya shigar kan Tinubu ranar Juma’a 19 ga watan Mayu.

Mai shari’a Haruna Tsammani, wanda ke jagorantar kwamitin mai mutane biyar ya bayyana cewa an ɗage shari’ar ne domin ci gaba da zaman sauraron ƙarar da kuma sauraron ɓukatun waɗanda aka yi ƙarar suka shigar.

Kotu ta ɗage ƙarar da Peter Obi ya shigar da Tinubu

Haka nan ma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta ɗage ƙarar da ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi ya shigar a kan Bola Tinubu.

Kotun dai ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar juma'a, 19 ga watan Mayu domin ƙara jin ta bakin shaidu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng