Kotun Zabe Ta Sake Dage Sauraron Karar Atiku Abubakar Kan Nasarar Tinubu, Ta Bayyana Sabon Lokaci
- Kotu ta sake ɗage sauraron ƙarar Atiku Abubakar kan nasarar Asiwaju Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa
- Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasar ta sanya ranar Juma'a 19, ga watan Mayu domin cigaba da zamanta
- A zaman kotun na ranar Juma'a za ta yanke yawan shaidun da za a gabatar mata domin cigaba da sauraron ƙarar
Abuja - Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta ɗage zamanta har sai zuwa ranar Juma'a, 19 ga watan Mayu, kan ƙarar da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya shigar.
Atiku Abubakar ya shigar da ƙara a gaban kotun zaɓen ne, domin ƙalubalantar nasarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Jaridar Vanguard ta yi rahoto cewa, kotun mai alƙalai biyar wacce mai shari'a Haruna Tsammani, ke jagoranta, ta ɗage sauraron cigaba da zaman fara sauraron ƙarar da jin ƙorafe-ƙorafen da waɗanda ake ƙara suka shigar.
Waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar dai sun haɗa da, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu da jam'iyyar All Progressives Congress, (APC).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da suke nema a kotu
Waɗanda ake ƙarar na neman kotun ta yi fatali da ƙarar gaba ɗayanta, ko ta soke da yawa daga cikin ƙorafe-ƙorafen da aka yi a cikin ƙarar saboda rashin cancantar su.
A yayin da ya ke ɗage ƙarar, mai shari'a Haruna Tsammani, ya ce kotun a ranar Juma'a za ta yanke ko shaidu nawa za a gabatar a gabanta, lokacin da za a ba kowannen su da kuma lokacin da za a bayar domi yin martani.
Ya buƙaci ɓangarorin da su yi aiki tare domin amincewa da sauran hanyoyin da yakamata kotun ta bi wajen gudanar da shari'ar.
Kotu Ta Sake Dage Karar Peter Obi Kan Nasarar Bola Tinubu
Rahoto ya zo cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, ta sake ɗage sauraron ƙarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya shigar kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Kotun ta ɗage zamanta domin sauraron ƙarar ne zuwa ranar Juma'a, 19 ga watan Mayun 2023.
Asali: Legit.ng