Osinbajo Ya Kamata APC Ta Tsayar Takara a Zaben 2023, Peter Obi
- Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya ce mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, yana da gogewar kawo canji a Najeriya
- Obi, ɗan takarar LP a babban zaben 2023, ya ce ya tunkari APC kan ta baiwa Osinbajo tikitin takarar idan har suna son ci gaban ƙasar nan
- A halin yanzun dai ya shigar kara gaban Kotu yana kalubalantar nasarar shugaban kasa mai jiran gado
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya ce APC zata iya haɓaka Najeriya idan da mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ta tsayar takara a zaben da ya wuce.
Punch ta rahoto cewa Obi ya yi wannan furucin ne yayin da yake gaisawa da manyan baƙin da suka halarci bikin cikar Dele Momodu shekara 63 a duniya wanda ya gudana a Landan.
Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini
A wani bidiyon daƙiƙa 52 wanda ya karaɗe kafafen sada zumunta, tsohon gwamnan Anambra ya yi ikirarin cewa ya taba tunkarar jam'iyyar APC kan wanda ya cancanta ya gaji shugaba Buhari.
Mista Obi ya ce ya gaya wa jam'iyyar APC cewa idan suna kaunar Najeriya ta dawo kan ganiyarta to su miƙa wa Osinbajo tikitin takarar shugaban ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Leadership ta rahoto Obi ma cewa:
"Ba zan ɓoye muku ba, naƙosa na ga Najeriya ta dawo kan ganiyarta. Har tunkararsu na yi na ce idan kuna son ci gaban ƙasar nan, me zai hana ku kawo Osinbajo?"
"Najeriya na buƙatar mutum mai lafiya wanda zai iya kwashe awanni 24 yana aiki bai gaji ba. Mu haɗu mu gina wurin da zai yi aiki domin kowa ya amfana."
Idan baku manta ba, Peter Obi ya shigar ƙara gaban Kotun zabe yana kalubalantar nasarar zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda INEC ta sanar.
Ɗan takarar LP ya zo a matsayin na uku a sakamakon zaben shugaban ƙasa wanda ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023. Atiku Abubakar na PDP ya zo na biyu.
Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Ganawarsa da Bola Tinubu a Faransa
A wani labarin kuma Kwankwaso Ya Yi Magana Mai Kyau Game da Rahoton Ganawarsa da Bola Tinubu a Ƙasar Faransa
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP ya ce zai yi cikakken jawabi idan Allah ya kaimu ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng