‘Yan Adawa Sun Baza Wuta, An Sake Shigar da Kara Domin Hana Tinubu Shiga Aso Rock

‘Yan Adawa Sun Baza Wuta, An Sake Shigar da Kara Domin Hana Tinubu Shiga Aso Rock

Wata kungiya mai suna ASRADI ta je kotu saboda ganin an tsaida batun rantsar da shugaban kasa

  • A matsayinsa na shugaban ASRADI, Adeolu Oyinlola ya fadawa kotu zargin da ake yi wa Bola Tinubu
  • Lauyan da ya shigar da kara a kotun tarayya mai zama a garin Abuja shi ne Chukwunweike Okafor

Abuja - Wata kungiya mai zaman kan ta mai suna ASRADI ta tafi kotun tarayya mai zama a garin Abuja a kan batun rantsar da Asiwaju Bola Tinubu.

Rahoton da aka samu daga Premium Times ya ce kungiyar ASRADI ta roki kotun tarayyar ta bada umarni fasa rantsar da zababben shugaban kasar.

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/669/2023, kungiyar ta ce Bola Tinubu ya yi wa hukumar INEC karya, ya mallaki katin zama ‘dan kasar Gambiya.

Kara karanta wannan

Babban Jigon APC Ya Faɗi Ɗan Takarar da Ba Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ba, Ya Faɗi Dalilai

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Yemi Osinbajo Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lauyoyin ASRADI sun shigar da kara su na masu rokon Alkali ya yi gaggawar yanke hukunci a kan shirin rantsar da sabon shugaban kasa da ake ta yi.

Ya kamata IGP ya yi bincike

Jaridar ta ce bayan neman a hana rantsuwa a ranar 29 ga watan Mayu, kungiyar mai zaman kan ta ta na so a tursasa ‘Yan sanda su binciki Bola Tinubu.

Idan Shugaban ‘yan sandan Najeriyan ya samu tsohon Gwamnan na jihar Legas da mallakar katin kasar Gambiya, ASRADI ta na so a gurfanar da shi.

Vanguard ta ce ASRADI ta sanar da kotu cewa shugaban mai jiran gado ya yi karya ne a wajen cike takardar EC9 da zai shiga takarar shugaban kasa.

"Kin bayyana gaskiyar Bola Ahmed Tinubu na zama cikakken ‘dan kasashe biyu a takardar EC9 ya na nuna ya yi rantsuwar karya."

Kara karanta wannan

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

- Adeolu Oyinlola

Idan ikirarin ya tabbata, Lauyan da ya tsayawa ASRADI ya ce sai a watan Afrilun nan suka samu wannan labari bayan ‘yan sanda sun ki binciken batun.

Ganin jami’an tsaro ba su yi abin da ya kamata ba, hakan ya jawo kungiyar ta sheka kotu.

Chukwunweike Okafor shi ne Lauyan da ya tsayawa Shugaban ASRADI, Adeolu Oyinlola. Zuwa yanzu ba a sa ranar da kotu za ta fara zama ba tukuna.

Ministoci da za su iya zarcewa

Lai Mohammed, Sunday Dare da Ade Mamora su na tare da Bola Tinubu tun ba yau ba, rahotonmu ya nuna irinsu za su iya cigaba da rike kujerun Ministoci.

Duk da ya yi shekaru kusan takwas a ofis, doka ba ta hana Tunde Babatunde Fashola SAN sake rike kujerar Minista ba, mu na hasashen zai iya zama sabon AGF.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng