Pantami da Wasu Ministocin Buhari 9 da Za Su Iya Tsira da Kujerunsu a Mulkin Tinubu
- A ‘yan kwanaki masu zuwa ne Shugaban Najeriya zai sauke daukacin Ministocin gwamnatinsa
- Watakila a cikin Ministocin kasar akwai wadanda Shugaba mai jiran gado, Bola Tinubu zai tafi da su
- Wasu Ministoci masu barin-gado sun yi shekaru bakwai a ofis, wasu kuma ba su kai shekara hudu ba
Abuja - A rahoton nan, Legit.ng Hausa tayi kokarin yin hasashe a kan Ministocin Tarayya da za su cigaba da rike mukamansa a sabuwar gwamnati.
1. George Akume
George Akume yana da kyakkyawar alaka da zababben shugaban kasa, ko da bai samu kujerar Minista ba, ana tunanin zai iya samun wata kujera a gwamnatin gobe.
2. Festus Keyamo
Festus Keyamo ya taka rawar gani wajen yakin neman zaben APC, ba abin mamaki ba ne a ga karamin Ministan kwadagon ya cigaba da rike matsayinsa ko waninsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
3. Isa Ali Ibrahim Pantami
Idan aka yi la’akari da kokarin da ya yi a ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani da kuma gudumuwar da ya bada a kamfe, Isa Pantami zai iya zarcewa.
4. Ramatu Tijani
Ana rade-radin Ramatu Tijjani ta na so ta rike kujerarta a gwamnati mai zuwa. Hakan zai iya yiwuwa domin sai a 2024 Yahaya Bello zai bar kujerar Gwamna a Kogi.
5. Lai Mohammed
Alhaji Lai Mohammed ya dade tare da Bola Tinubu, watakila ya nemi wani mukami ya ba shi a kujerar jihar Kwara, matsalar kurum ita ce Ministan yana da shekara 71.
6. Olorunnimbe Mamora
Kafin karbar mukami a gwamnatin Muhammadu Buhari, Olorunnimbe Mamora ya yi Sanata a Legas, kuma yana cikin wadanda sun dade da sanin Tinubu a siyasa.
7. Sunday Dare
Idan ana maganar na-kusa da zababben shugaban Najeriyan kafin yau akwai Sunday Dare, watakila a gwamnati mai zuwa a canzawa Ministan matasan ma’aikata.
8. Adeniyi Adebayo
Wani da mu ke ganin zai iya samun shiga bayan shudewar gwamnatin nan shi ne Ministan harkokin kasuwanci, masana'antu da hannun jari, Adeniyi Adebayo.
9. Babatunde Fashola
Ko da ya dade yana rike da mukamin Minista, wasu su na hangen Babatunde Fashola a kujerar Ministan shari’a, a matsayinsa na SAN zai iya zama lauyan gwamnati.
10. Abdulrahman Bello Dambazau
Na karshe a jerin shi ne Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya. Duk da ya rasa kujerarsa a 2019, ana ganin tsohon sojan yana tare da shugaba mai jiran gado.
Cikas a gaban Tinubu
A rahoton da mu ka fitar, an ji cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana shirin karbar mulkin Najeriya a lokacin da ake fama da rashin aikin yi da tsadar kayan abinci.
Tinubu zai nemi cire tallafin man fetur amma hakan zai haifar da tsadar rayuwa. Daga cikin abubuwan da za su ba ciwon-kai akwai samar da isasshen lantarki.
Asali: Legit.ng