‘Yan PDP, LP da NNPP Fiye da 100 Su Na Goyon Bayan ‘Dan Takaran APC a Majalisa
- Akwai 'ya 'yan jam’iyyun PDP, LP, NNPP da sauran masu adawa da sun hada-kai da APC a Majalisa
- Zuwar Lahadin da ta gabata, lissafi ya nuna jam’iyyar APC ta na da marasa rinjaye 107 a tare da ita
- Hon. Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu sun samu karin goyon bayan Gwamnonin jihohi
Abuja - Tajuddeen Abbas mai neman zama shugaban majalisar wakilan tarayya ya ce akwai abokan aikinsa daga jam’iyyu hamayya da ke tare da shi.
Yayin da Hon. Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu suka ziyarci Gwamna Simon Lalong, Vanguard ta rahoto ‘dan majalisa ya yi maganar karbuwarsa.
‘Dan majalisar mai wakiltar Zaria ya fadawa Gwamnan Filato cewa zababbun ‘yan majalisa akalla 107 daga jam’iyyun adawa suke marawa takararsa baya.
An yabi aikin Simon Lalong a zabe
Hon. Tajuddeen Abbas, Hon. Ben Kalu da Hon. Bello Kumo sun jinjinawa irin kokarin da Simon Lalong ya yi a zaben shugaban kasar da aka shirya a bana.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An yabi Lalong ganin yadda ya rika tallata tikitin Musulmi da Musulmi da jam’iyyar APC ta yi.
Rahoton ya ce Abbas da Kalu sun shaidawa Gwamnan cewa su na takara ne domin hada-kan al’ummar kasa, biyayya da kuma kawo zaman lafiya a mulki.
Alfarmar da ‘yan majalisar suke nema shi ne Mai girma Lalong ya mara masu baya a zaben da za ayi a majalisar wakilan tarayya nan da ‘yan kwanaki kadan.
"Mu na da jama’a daga cikin duka jam’iyyun siyasa takwas. Kuma zan iya bugun kirji in fada maka zuwa Lahadi, mu na da marasa rinjaye 107 tare da mu."
- Hon. Tajuddeen Abbas,
This Day ta ce Lalong ya fara jawabinsa da taya zababbun ‘yan majalisar murnar lashe zaben 2023 da suka yi, ya ce akwai bukatar samun hadin-kai a kasa.
Lalong ya na da bukata
Mai girma Gwamnan ya roki ‘yan takaran da cewa ka da su manta da yankinsa na Arewa maso tsakiya idan sun yi nasarar lashe zaben da za ayi a Yuni.
Shi ma Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna yana goyon bayan Abbas/Kalu, ya yi watsi da mutumin jiharsa, Mukhtar Betara.
Gwamnan ya nuna haka a sa’ilin da Hon. Usman Bello Kumo suka kai masa ziyara a Abuja. Shi ma Gwamnan Bauchi bai nuna zai yaki APC mai rinjaye ba.
Kuskuren 2015 ba zai maimaitu ba
A zaben shugabannin majalisar tarayya ta 10 da za ayi a farkon watan Yuni, an samu labari APC ta ce sai an yi hattara da abin da ya faru lokacin zaben 2015.
Bukola Saraki da Ike Ekweremadu sun koyawa jam’iyyar APC darasin da ba za ta manta ba, APC NWC ta ce dole Godswill Akpabio sai ya yi da gaske.
Asali: Legit.ng