Kwamitin Aikace-Aikacen APC Na Ganawa Da Sanatoci Kan Matsalolin Da Suka Tunkaro Jam'iyyar

Kwamitin Aikace-Aikacen APC Na Ganawa Da Sanatoci Kan Matsalolin Da Suka Tunkaro Jam'iyyar

  • Jam’iyyar APC na ƙoƙarin ɗinke ɓarakar da ta kunno kai cikinta biyo bayan tsarin shugabancin majalisa ta 10 da ta yi a makon da ya gabata
  • Sanata Godswill Akpabio da Barau Jibrin sun gana da kwamitin ayyuka na jam'iyyar APC ta ƙasa domin tattaunawa kan matsalar
  • Kwamitin aikace-aikace na jam'iyyar ta APC ya yi alƙawarin yin gyare-gyare da suka dace a dangane da batun shugabancin majalisar

Abuja - Alamu na nuni da cewar jam’iyyar APC na ƙoƙarin magance rikicin da ya ɓarke a cikinta, sakamakon tsarin shugabancin majalisa ta 10 da ta yi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a wani mataki na sasanta rikicin da ya ɓarke, a yanzu haka Sanata Godswill Akpabio da Barau Jibrin na ganawa da kwamitin gudanarwar jam’iyyar na ƙasa.

Akpabio, Barau
Akpabio, Barau Na Ganawa Da Kwamitin Aikace-Aikacen Na APC Kan Matsalolin Da Suka Tunkuro Jam'iyyar. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Sama da sanatoci 40 suka halarci taron

Kara karanta wannan

Rikicin Jam'iyya: An Dakatar Da Tsohon Shugaban PDP na Ƙasa? NWC Ta Yi Bayani Kan Hukuncin

Taron wanda ke gudana a gidan Muhammadu Buhari wanda shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu ke jagoranta, ya samu halartar Sanatoci sama da 40 da suka haɗa da Godswill Akpabio da kuma Barau Jibrin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar The Nation ta wallafa cewa sanatocin sun isa gidan Muhammadu Buhari da misalin karfe 12:55 na ranar Talatar nan.

APC ta fitar da shuwagabanin majalisu

A kwanakin baya ne dai jam’iyyar ta APC ta sanar da waɗanda ta ke so su jagoranci tagwayen majalisun; wato ta dattawa da ta wakilai.

Hakan dai ya biyo bayan wata tattaunawa da suka yi da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

APC ta dame kan batun shugabancin majalisa

Sai dai kuma abin bai yiwa wasu daga cikin ‘ya’ yan jam’iyyar ta APC daɗi ba, inda suka nuna rashin amincewarsu kan yadda shugabannin jam’iyyar suka gudanar da lamarin, inda kuma suka sha alwashin kawo cikas a lokacin zaɓe.

Kara karanta wannan

Dan Majalisar APC Ya Hango Wani Babban Kuskure Da Jam'iyyar Za Ta Yi Kan Shugabancin Majalisa ta 10

A wani zama da suka yi, kwamitin aikace-aikace na jam'iyyar ya tabbatarwa da fusatattun 'yan majalisun cewa za a yi gyare-gyare kan matsayar da jam'iyyar ta ɗauka.

Yan adawa za su iya karɓe shugabancin majalisa

A wani labarin mu na baya, mun kawo muku cewa wasu daga cikin 'yan majalissun jam'iyyun adawa na yunƙurin mamayar jam'iyya mai mulki wajen ƙwace shugabancin majalissun.

Hakan dai ya biyo bayan rikicin cikin gida da ke addabar jam'iyyar ta APC dangane da shugabancin tagwayen majalissun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel