"Babban Kuskure Ne Idan APC Ta Watsar Da Yankin Kudu Maso Gabas a Shugabancin Majalisa", Kalu

"Babban Kuskure Ne Idan APC Ta Watsar Da Yankin Kudu Maso Gabas a Shugabancin Majalisa", Kalu

  • Benjamin Kalu ya ankarar da jam'iyyar APC kan wani gagarumin kuskure da jam'iyyar za ta yi kan shugabancin majalisa ta 10
  • Ɗan majalisar wanda jam'iyyar ta zaɓa a matsayin mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya ce akwai kuskure idan ba a dama da yankin Kudu maso Gabas ba
  • Kalu ya ce a halin da ake ciki yanzu kamata ya yi a dama da kowane yanki a shugabancin majalisa ta 10

Abuja - Zaɓin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a kujerar mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya yi ƙarin haske kan dalilin jam'iyyar na kai kujerar yankin Kudu maso Yamma.

Ɗan majalisar mai wakiltar Bende daga jihar Abia a majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne a cikin shirin Channels tv na Sunday Politics.

Babban kuskure ne cire yankin Kudu maso Gabas a shugabancin majalisa ta 10, cewar Kalu
Benjamin Kalu ya ankarar da jam'iyyar APC kan shugabancin majalisa ta 10 Hoto: Channels Television
Asali: Twitter

Kalu yana da ra'ayin cewa yakamata APC ta dama da yankin na Kudu maso Gabas domin kada ta ƙara samun rashin ƙuri'u a yankin a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Babban Jigon APC Ya Faɗi Ɗan Takarar da Ba Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ba, Ya Faɗi Dalilai

Da ya ke magana kan watsi da matsayar jam'iyyar na kai kujerar yankin da wasu daga ƴan takarar kujerar kakakin majalisar suka yi, Kalu yace jam'iyyar na son haɗa kan ƙasa ne, shiyasa ta ɗauki wannan matakin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa yankin na Kudu maso Gabas bai riƙe wata kujera mai gwaɓi ba a majalisa ta tara, inda ya ƙara da cewa babbar kasada ce ga jam'iyyar APC idan ba ta ba yankin wata kujera mai gwaɓi ba a majalisa ta 10, cewar rahoton The Cable.

A kalamansa:

"Abinda ya bambanta gwamnatin da mu ke tsammani daga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, shine ya san muhimmancin tafiya da kowa. Abinda zai faru a zaɓen shekarar 2027 zai fara ne daga abinda muka yi a yanzu."
"Idan ana maganar gina ƙasa, mantawa ake da son zuciya, mantawa ake da bambance-bambance, sai a yi duba zuwa ga abinda yafi dacewa da a yi, inda a yanzu abinda yafi dacewa ayi shine yadda za mu tafi da kowa a shugabancin majalisa."

Kara karanta wannan

Majalisa ta 10: Daga Karshe Gwamnonin APC Sun Shirya Kawo Mafita Kan Rigimar Shugabancin Majalisa

Ɗan majalisar ya ce idan aka dama da yankin na Kudu maso Gabas, tabbas jam'iyyar za ta ribaci hakan a nan gaba.

Dalilin da Yasa Orji Kalu Ba Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa Ba, Adamu

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Adamu Garba, ya yi tsokaci kan takarar shugabancin majalisar dattawa ta 10 na sanata Uzor Kalu.

Adamu ya nuna cewa Kalu ba zai iya samun nasara ba a takararsa saboda rashin kataɓus ɗin da jam'iyyar APC ta yi a yankinsa na Kudu maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng