Kotu Ta Bijiro Da Sabbin Batutuwa Yayin Da Mazauna Abuje Ke Neman Su Hana Rantsar Da Tinubu

Kotu Ta Bijiro Da Sabbin Batutuwa Yayin Da Mazauna Abuje Ke Neman Su Hana Rantsar Da Tinubu

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta buƙaci mazauna babban birnin tarayya Abuja da su zo su yi bayani kan karar da suka shigar ta neman a dakatar da rantsar da Bola Tinubu
  • Mazauna yankin Abuja dai na neman a yi duba zuwa ga sashe na 134 (2) na kundin tsarin mulkin ƙasa, kan batun dan takarar da bai cika sharuddan kashi 25 na kuri'un da aka kaɗa a babban birnin tarayya Abuja ba
  • Sun kuma nemi kotu ta hana alƙalin alƙalai na ƙasa ko wani ma'aikacin hukumar shari'a da ke da iko daga rantsar da duk wani ɗan takarar da bai cika sharuɗan da sashe na 134 (2) ya gindaya ba

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci mazauna birnin tarayya da su yi ma ta bayani kan koken da suka shigar na neman hana rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Fitacciyar Kasuwa, An Yi Asarar Dukiya

Mai shari’a Inyang Ekwo, ya nemi mazauna birnin tarayya da masu kaɗa kuri’a su yi wa kotu bayani kan matsaya da kuma huruminsu a kan batun.

Haka nan kuma kotun ta nemi su faɗa ma ta cewa ko akwai makamancin irin wannan batu a gaban kotun sauraron ƙarar zaben a baya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Bola Tinubu/Zaben Shugaban Kasa/Kotu
Kotu ta ce mazauna Abuja su taho su yi bayanin abin da yasa suke son hana rantsar da Tinubu. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Sun nemi kotu ta yi musu kashin baki kan doka

Tun da farko, lauyan mazauna babban birnin tarayya Abuja, Chuks Nwachukwu Esq, ya shaidawa kotun cewa sun shigar da karar ne tun a baya inda suka nemi kotu ta yi musu fashin-baƙi kan abinda dokar ta ce.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mazauna yankin na neman karin bayani kan sashe na 134 (2) (b) na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya ke magana kan ɗan takarar shugaban ƙasa da bai cika sharuɗan samun kashi 25 cikin 100 na kuri'un Abuja ba.

Kara karanta wannan

Yanzu - Yanzu: Mazauna Abuja Sun Maka Tinubu A Kotu Don Hana Rantsar Da Shi, Lauya Ya Yi Martani

Mazaunan na birnin tarayya sun samu wakilcin Anyaegbunam Ubaka Okoye, David Aondover Adzer, Jeffrey Oheobeh Ucheh, Osang Paul da Chibuke Nwachukwu wajen shigar da ƙarar.

Suna son kotu ta haramtawa alkalin alkalai rantsar da Tinubu

Sun nemi kotu ta haramtawa alƙalin alƙalan Najeriya da duk wani jami’in shari’a ko wata hukuma ko wasu mutane damar rantsar da kowane ɗan takara a zaben shugaban kasa na da ya gabata.

Haka nan kuma, sun buƙaci kotu ta bada umarnin dakatar da duk wata sanarwa ko bayar da takardar shedar cin zaɓe ga kowane ɗan takara a zaben shugaban ƙasa da ya gabata.

Daga ƙarshe dai alƙalin da ke sauraron ƙarar ya ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 18 ga watan Mayu da muke ciki.

An tsige hadimai 18 a wata ma'aikatar gwamnatin tarayya

A wani labarin kuma, kotu ta tsige hadimai 18 a ma'aikatar kula da jin dadin 'yan Neja-Delta wato NDDC.

Kotun ta ce mutanen da aka tsige na cikin wadanda aka dauka ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng