Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

  • Olusegun Mimiko ya gabatar da jawabi a taron da Gidauniyar Dare Adeboye ta shirya a makon jiya
  • ‘Dan siyasar ya ba Gwamnati mai zuwa shawarar ta fara da dabbaka alkawuran da ta dauka da kan ta
  • Mimiko yana ganin dole a canza tsarin aikin ‘yan sanda da fasalin kasa, a kuma cire tallafin man fetur

Ondo - Olusegun Mimiko wanda ya yi mulki a jihar Ondo, ya yi wasu kiraye-kiraye zuwa ga zababben shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu.

Gidauniyar Dare Adeboye ta shirya lacca domin nuna inda ya dace gwamnati mai zuwa ta sa gaba, Sun ta ce Olusegun Mimiko ya yi jawabi a taron.

Segun Mimiko ya ba Asiwaju Bola Tinubu shawarar ya maida hankali wajen kirkiro jami’an tsaro a jihohi, sannan a ragewa gwamnatin tarayya iko.

Kara karanta wannan

Akwai Kudi: Gwamnati Na da Arzikin Karawa Ma’aikata Albashin da Ake Biya Inji Minista

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Muhammadu Buhari a Legas Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tsohon Gwamnan ya ce babu babban kalubalen da ke gaban Gwamnatin da za ta gaji mulki irin hada-kan kabilu da bangarorin da ake da su a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aiki a gaban Gwamnatin Tinubu

Mimiko ya ce ya zama dole gwamnatin Tinubu ta fara da kallon sha’anin ‘yan sandan jihohi, kason albarkatun kasa, da kuma cire tallafin man fetur.

Haka zalika an rahoto ‘dan siyasar yana cewa akwai bukatar a duba yadda za a samar da ayyukan yi, kuma a gyara tsarin takaita yawon kudi.

A ra’ayin Mimiko, sai Jihohi sun samu ‘yan sandan kansu za magance rashin tsaro.

Tattalin arzikin Najeriya

Jaridar Leadership ta ce ‘dan siyasar ya yi kira ga gwamnatin da za a kafa a ranar 29 ga watan Mayu ta kawo tsare-tsare na inganta tattalin arziki.

Mimiko ya ce bai kamata Tinubu ya yi koyi da Muhammadu Buhari ba, kyau ya rika tafiya da kowa a wajen rabon mukaman gwamnati a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Yawaita Zuwa Turai: Tinubu zama zai yi ya mulki Najeiya, inji hadiminsa

Kamar yadda yake cikin alkawuran jam’iyyar APC, Mimiko yana ganin har jam’iyyun siyasa sun yi na’am da a kara karfi da iko ga gwamnonin jihohi.

Ganin bankin Duniya ya ce 96% na abin da ya shiga aljihun gwamnati ya tafi wajen biyan bashi ne, Mimiko ya ce dole a janye tsarin tallafin man fetur.

Akwai kudin karin albashi

A rahoton da mu ka fitar a baya, an ji cewa ana ganin karin albashin da aka yi wa wasu ma’aikata tamkar tarko aka shiryawa Bola Tinubu a mulki.

Ministan kwadago, Festus Keyamo SAN ya nuna ba za a ce babu dalilin fito da sabon tsarin albashi ba, lura da yanayin da mu ke rayuwa yau a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng