'Dan Shugaba Obasanjo Ya Fadi Wadanda Suka Dace da Shugabancin Majalisar Tarayya
- Olujonwo Obasanjo ya na tallata takarar da Godswill Akpabio yake yi a majalisar dattawa na kasa
- Yaron tsohon shugaban na Najeriya ya ce tsohon Gwamnan ya cancanci ya gaji Ahmad Lawan
- A zaben majalisar wakilan tarayya, Olujonwo Obasanjo ya na tare da zabin APC, Tajudeen Abass
Abuja - Olujonwo Obasanjo wanda jagora ne a jam’iyyar APC, ya shiga cikin masu goyon bayan takarar Godswill Akpabio a majalisar dattawa.
Rahoton Premium Times ya nuna yaron tsohon shugaban na Najeriya ya goyi bayan Sanata Godswill Akpabio ya gaji kujerar Dr. Ahmad Lawan.
Haka zalika a zaben da za ayi a majalisar wakilan tarayya, Olujonwo Obasanjo ya na tare da Hon. Abbas Tajudeen wanda jam’iyyarsa ta ayyana.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar da ta gabata, Obasanjo ya yi kira ga zababbun ‘yan majalisar tarayya su yi wa jam’iyya biyayya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Dan siyasar ya ce Akpabio ya cancanci ya shugabanci ‘yan majalisar dattawa saboda irin biyayyar da ya nuna ga APC da zababben shugaban kasa.
Ana ganin girman Akpabio
"Akpabio ya saye fam din neman takarar shugaban kasa, amma a daren zaben tsaida gwani, sai ya janyewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
Shugabannin jam’iyyar APC, zababben shugaban Najeriya, da duka sauran masu ruwa da tsaki su na ganin girman Sanata Godswill Akpabio.
- Olujonwo Obasanjo
Saboda haka ana matukar maraba da ayyana shi a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa.
Kamar yadda tsohon Gwamnan na Akwa Ibom ya cancanta, an rahoto Obasanjo yana cewa Abbas Tajudeen zai dace da shugaban majalisar wakilai.
Daga Gbaja sai Taju - Obasanjo
“Tajudeen Abass ya yi namijin kokari wajen bada gudumuwar kawo dokoki a majalisa, wannan kurum ya isa ya sa ya zama shugaban majalisa.
Wannan Basarake na kasar Zazzau ya yi zarra wajen harkar kawo dokoki, shi kadai ya kawo kudiri 74, a cikinsu shugaban kasa ya sa hannu a 21.
- Olujonwo Obasanjo
Akpabio ya yi karfi
An rahoto tsohon Gwamnan Akwa Ibom watau Godswill Akpabio ya ce Sanatoci kusan 70 ke goyon bayan shi, kuma za su iya kai 86 kafin zabe.
Godswill Akpabio ya ce ana amfani da kudi a zaben bana, ya ce Majalisar dattawa kunshe ta ke da masu daraja da ba za su bari a saida kasar ba.
Asali: Legit.ng