"Yanzu Lokaci Na Ya Yi": Mai Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ya Bijirewa APC Da Tinubu

"Yanzu Lokaci Na Ya Yi": Mai Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ya Bijirewa APC Da Tinubu

  • Idris Waje mai neman kujerar shugabancin majalisar wakilai, ya bijirewa matsayar jam'iyyar APC kan shugabancin majalisar
  • Wase wanda mataimakin kakakin majalisar wakilan ne ya bayyana cewa yanzu lokacinsa ya yi da zai zama kakakin majalisar
  • Wase ya yi nuni da cewa yankin da ya fito na Arewa ta tsakiya bai taɓa samun kujerar kakakin majalisar wakilai ba

Abuja - Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase, ya bijirewa matsayar jam'iyyar APC na kai takarar kujerar majalisar yankin Arewa maso Yamma, inda ya bayyana a hukumance yana neman shugabancin majalisar.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa, da ya ke magana wajen ayyana takararsa a otal ɗin Transcorp, a birnin tarayya Abuja, ya kwaikwayi Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa yanzu lokacinsa ne.

Wase ya bayyana kudirin zama kakakin majalisar wakilai
Ahmed Idris Wase, mataimakin kakakin majalisar wakilai Hoto: Punch.com
Asali: UGC

A kalamansa:

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

"A wannan gaɓar, zan yi amfani da kalaman shugabana Bola Tinubu, emi lokan, emi lokan, emi lokan"

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idris Wase, wanda ya fito daga jihar Plateau, ya bayyana cewa dole ne jam'iyyar APC, ta yi amfani da kundin tsarin mulkin Najeriya wajen tabbatar da cewa ba a ware yankin Arewa ta tsakiya ba, wajen rabon muƙamai duk da cewa kundin bai yi magana kan yadda za a raba muƙaman ba.

"Yana da kyau a lura da cewa yankin Arewa ta tsakiya ne kawai bai taɓa samar da kakakin shugaban majalisar wakilai ba, a shekara 24 da aka yi bayan an dawo mulkin Dimokuraɗiyya a shekarar 1999." A cewarsa.

Wase yana ɗaya daga cikin ƴan majalisar da ke kan gaba wajen bijirewa tsarin jam'iyyar kan kujerun shugabancin majalisa. Sauran sun haɗa da Alhassan Doguwa, Muktar Betara, Sada Soli da Aminu Wali, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Daga Buhari Zuwa Dogara: Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Majalisar Wakilai Tun 1999 Zuwa Yanzu

Fusatattun ƴan majalisar waɗanda suka nuna aniyar su ta neman shugabancin majalisar wakilai, sannan sun haɗa wata ƙungiya mai suna Coalition of Progressive Speakership Aspirants (COPSA).

Dalilin da Yasa Muka Zabi Akpabio a Abbas a Matsayin Shugabannin Majalisa, Shettima

A wani rahoton na daban kuma, zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana dalilin da ya sanya jam'iyyar ta zaɓi Akpabio da Abbas, a matsayin shugabannin majalisa.

Shettima ya bayyana zaɓin na su, ya biyo bayan son kawo daidaito da zaman lafiya a ƙasa da jam'iyyar ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng