Jerin Gwamnonin PDP Da Suka Kauracewa Taron Haɗuwa da Atiku Abubakar
Yunkurin babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa PDP na fara haɗa kan mambobinta da suka fusata ya gamu babban cikas ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, 2023.
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya yi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya haɗa Atiku Abubakar, gwamna Ifeanyi Okowa da gwamnonin G-5 a wuri ɗaya amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.
The Nation ta rahoto cewa gwamnonin G-5 ba su halarci liyafar da ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP ta shirya jiiya Alhamis ba a birnin tarayya Abuja.
An yi tsammanin taron zai haɗa Atiku, abokin takararsa, gwamna Okowa da sauran jiga-jigan jam'iyyar wuri ɗaya, wanda hakan ka iya zama matakin farko na sasantawa da juna.
Jerin gwamnonin da ba su halarci wurin ba
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa ƙungiyar gwamnonin PDP ta shirya taron ne domin zababbun gwamnoni da waɗanda suka zarce, amma ta gayyaci dukkan masu ruwa da tsaki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mun haɗa muku sunayen gwamnoni 6 da kuma zababben gwamna ɗaya da suka kauracewa liyafar, ga su kamar haka;
1. Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas
2. Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo
3. Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai
4. Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abiya
5. Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu
6. Gwamna mai jiran gado, Simi Fubara, na jihar Ribas (Magajin Wike)
7. Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom.
Shin an gayyaci gwamnonin?
Bayanai sun nuna cewa Tambuwal ya aike da katin gayyata ga baki ɗaya mambobin G-5 karkashin jagorancin gwamna Wike amma suka yi fatali da zuwa taron.
Haka zalika babu wanda ya tura wakili amma zababben gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya halarci taron wanda ya gudana a Transcorp Hilton Hotel, Abuja,
Zababben gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Bassey Eno, bai samu zuwa ba amma ya tura wakilcin mataimakinsa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A wani labarin kuma Kwana 17 Gabanin Miƙa Mulki, Gwamnan PDP Ya Kaddamar da Aikin da Ba'a Gama Ba
Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya baiwa kowa mamaki yayin da ya kaddamar da rukunin gidaje har ya rada masa suna amma ba'a kammala ba.
Rahoto ya nuna gwamnatin Taraba ta fara aikin tun a 2017 amma har yanzu a watan Mayu, 2023 ba'a kammala gina gidajen ba.
Asali: Legit.ng