Gwamna Adeleke da Wasu Gwamnoni 4 da Suka Yi Nasara a Kotu

Gwamna Adeleke da Wasu Gwamnoni 4 da Suka Yi Nasara a Kotu

Siyasar Najeriya musamman zabubbuka a kasar mafi akasari na zuwa ne da abubuwan mamaki da ba zata da kuma rashin daidaito a mafi yawancin lokuta tun dawowar dimukradiya a shekarar 1999.

Shekaru da dama, kasar ta gudanar da zabubbuka kuma mafi yawancin sakamakon zabubbukan na zuwa ne ba yadda wasu bangarori suka so ba, saboda haka ake zuwa kotu inda ake shafe watanni ko shekaru ana shari’a.

adeleke
Gwamna Adeleke, Hoto: Punch
Asali: Facebook

Kamar yadda Punch.ng ta tattaro, jiya Tarata 9 ga watan Mayu ne gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya yi nasara akan abokin karawarsa na APC, Gbenga Oyetola, bayan da kotun koli ta tabbatar masa da kujerarsa.

Ga jerin sunayen gwamnoni 5 da suka yi nasara a kotu bayan faduwarsu:

Ademola Adeleke, Jihar Osun

A watan Yuli na shekarar 2022, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke ya samu nasarar zama gwamnan jihar Osun.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Kotun Koli Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Ci Zaben Gwamnan Osun

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanata Ademola ya samu kuri’u 403,371 akan abokin hamayyarsa, Gbenga Oyetola na jam’iyyar APC wanda bai yarda da sakamakon zaben ba.

Oyetola ya garzaya kotu da korafe-korafe da suka hada da zargin cewa takardun makarantar Sanata Ademola na bogi ne.

Bayan mai shari’a Tersea Kume ta tabbatar da rashin ingancin zabensa da bada umarni ga INEC ta sake zabe, Sanata Ademola ya daukaka kara zuwa kotun koli in da a jiya Talata 9 ga watan Mayu, kotun ta tabbatar dashi a matsayin sahihin zababben gwamna.

Ogbeni Rauf Aregbsola, Jihar Osun

Bayan shafe shekaru uku suna shari'a a kotu, Rauf Aregbesola na jam’iayyar ACN ya samu nasara a karshe.

A shekarar 2007 aka sanar da Olagunsoye Oyinlola a matsayin zababben gwamnan jihar Osun, sai Mista Aregbesola ya dangana zuwa kotu da hujjoji masu gamsarwa fiye da 100, bayan ya gabatar da korafe-korafe da dama.

Kara karanta wannan

Cikakken Jerin Sunayen Manyan Alƙalai 5 da Zasu Jagorancin Shari"a Kan Zaben Tinubu a 2023

Kayode Fayemi, Jihar Ekiti

Bayan sanar da Olusegun Oni a matsayin gwamnan jihar Ekiti a shekarar 2007, Kayode Fayemi na jam’iyyar ACN ya kalubalanci sakamakon zaben inda ya dangana zuwa kotu.

Bayan shafe fiye da shekaru 3 suna kotu akan sahihancin sakamakon zaben, kotun daukaka kara ta sanar da Kayode Fayemi a matsayin zababben gwamnan jihar ranar 15 ga watan Oktoba ta shekarar 2010 a kotun da ke zamanta a jihar Kwara.

Hope Uzodimma, Jihar Imo

A shekarar 2019, Gwamna Hope Uzodinma ya kalubalanci sakamakon zaben gwamnan jihar Imo bayan da hukumar zabe ta sanar da Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.

Uzodinma wanda ya zama na hudu a jerin 'yan takaran, ya daukaka kara zuwa kotu kafin a sanar da shi a matsayin halastaccen wanda ya lashe zabe a ranar 14 ga watan Janairu na shekarar 2019 bayan shafe watanni ana shari’a.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Tinubu Ya Ayyana Wadanda Yake So, Yari Ya Ce Zababben Shugaban Kasar Ya Yi Kadan

Ayo Fayose, Jihar Ekiti

Ayodele Fayose ya kalubalanci kashe zabensa da aka yi a matsayin gwamnan jihar da ya gudana a shekarar 2014.

Jam’iyyar da ta sha kaye wato APC wadda Kayode Fayemi ke wa takara tashigar da kara zuwa kotu kan cewar Fayose ya yi amfani da takardun bogi.

A ranar 16 ga watan Fabairu na shekarar 2015 ne kotun koli ta tabbatar da Fayose a matsayin halastaccen gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 21 ga watan Yuni na shekarar 2014.

Abubuwa 5 Masu Muhimmanci Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sanata Ike Ekeweremadu Da Matarsa

A wani labarin, Legit ta tattaro cewa kasashen ketare nan gida Najeriya na fakon Ekweremadu bayan ‘yan sandan Burtaniya sun kama bisa zargin da ake masa na safarar yara da siyar da wani bangare na sassan jikin wani matashi.

Sanata Ike Ekweremadu ya sha gwagwarmayar rayuwa sosai, a nan zamu duba abubuwa biyar da baku sani ba game da Sanatan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel