Abin da ‘Yan Takaran Kujerun Majalisa Su ka Fadawa Shugaban Jam’iyyar APC Gar da Gar

Abin da ‘Yan Takaran Kujerun Majalisa Su ka Fadawa Shugaban Jam’iyyar APC Gar da Gar

  • Yusuf Gagdi; Mukhtar Aliyu Betara; Ahmed Idris Wase; Hon. Sada Soli sun zauna da APC NWC
  • ‘Yan G7 da ke neman kujerar majalisar wakilai sun ja-kunnen APC, sun ce ba za su yi biyayya ba
  • Rt. Hon. Alhassan Doguwa, Hon. Mariam Onuoha, da Aminu Sani Jaji sun halarci taron da aka yi

Abuja - Mutum bakwai da ke cikin masu neman zama shugaban majalisar wakilan tarayya sun bar sakatariyar jam’iyyar APC a fusace a ranar Laraba.

Rahoton da Daily Trust ta fitar ya nuna ‘yan takaran ba su ji dadin yadda uwar jam’iyya ta kebe yankunan da shugabannin majalisa za su fito ba.

A zaman da aka yi da shugabannin jam’iyyar APC na kasa, wadannan ‘yan majalisa bakwai da ke harin shugabanci sun zargi NWC da yin rashin adalci.

Kara karanta wannan

Ba a Haka: Inda Tinubu Ya Yi Kuskure Wajen Shugabancin Majalisar Dattawa – Sanata

Majalisa
Wasu 'Yan Majalisa a bakin aiki Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

‘Yan majalisar tarayyar sun nuna za su yaki duk wani yunkuri da za ayi daga waje da nufin a kakaba masu wanda zai zama shugaban majalisa ta goma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tribune ta ce ‘yan majalisa sun fadawa jam’iyyar ba za su yarda da kason da aka yi masu ba.

"Ba haka ya kamata ba" - Gagdi

Hon. Yusuf Gagdi ya nanatawa Sanata Abdullahi Adamu, NWC tayi kuskure domin majalisar tarayya ba FEC ba, ta na zaman kan ta ne a tsarin mulki.

A jawabin da ya yi, Gagdi ya fadawa shugaban na APC cewa a ranar da majalisa za ta zabi shugabanninta, bai nan saboda haka, a guji yi masu shisshigi.

"Ya kamata a gyara kuskuren. Muddin ba ayi haka ba, ka da jam’iyya tayi tsammanin samun biyayyarmu alhali ba ayi adalci, gaskiya da neman zaman lafiya ba.

Kara karanta wannan

Akwai Yiwuwar Messi Ya Koma Wasa a Saudi a Cinikin da Zai Girgiza Duniyar Kwallo

Ran ka ya dade, ka da ka sa ran mun zo nan ne domin karbar wani umarni da za a ba mu.
Taken jam’iyyarmu ita ce adalci, zaman lafiya da hadin-kai. A karkashin jagorancinka, ka zura idanu an yi amfani da ‘yan jam’iyya, an tsaida mana ‘dan takaran shugaban kasa.
Mataimakin shugaban kasa ya yi takara; shi ya fi kowa kusanci da shugaban kasa, amma saboda damukaradiyya ake yi da adalcin APC, aka bar masu zabe su ka zabi ra’ayinsu.

- Yusuf Gagdi

Gagdi ya ce duk da adadin Kiristocin da ke Arewa ta tsakiya, amma APC tayi nasara a yankin a 2023, sai kuma a hana su mukami, a fifita Arewa maso yamma.

Akeredolu ya ce akwai rashin adalci

Rahoto ya zo cewa Shugaban kungiyar Gwamnonin Kudu maso yamma, Rotimi Akeredolu ya ce Bola Tinubu ake neman jefawa a rami a zaben majalisa.

Akeredolu ya koka kan Arewa maso yamma zai samu fifiko a wajen zaben shugabannin majalisa, alhali Arewa ta tsakiya ba za ta samu komai ba.

Kara karanta wannan

Lauyan Abba Gida-Gida Ya Yi Maganar Yiwuwar Samun Nasarar APC da Gawuna a Kotu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng