Ba a Haka: Inda Tinubu Ya Yi Kuskure Wajen Shugabancin Majalisar Dattawa – Sanata
- Ifeanyi Ubah ya zargi Asiwaju Bola Tinubu da yi wa majalisar dattawa katsalandan a sha’aninsu
- Sanatan Kudancin jihar Anambra ya na ganin bai dace ayi wa Sanatoci karfa-karfa a kan kujerarsu ba
- Sanata Ubah ya ce kyau a zauna da ‘yan majalisa kafin jam’iyya mai-ci ta kasa yadda za a raba mukamai
Abuja - Sanatan Najeriya, Ifeanyi Ubah ya soki zababben Shugaban kasa, Bola Tinubu da jam’iyyar APC saboda tsoma baki kan lamarin majalisa.
Da aka tattauna da shi a tashar Channels a ranar Litinin, Sanata Ifeanyi Ubah ya ce bai kamata Shugaban kasa mai jiran gado ya yi masu katsalandan ba.
‘Dan majalisar da ya sake lashe zabe a karkashin jam’iyyar YPP ya nuna Tinubu bai zauna da su kafin ya amince da yadda APC ta yi kason kujerunsu ba.
Ba haka ake yi ba
"Ba za ka yi amfani da karfi wajen wadannan abubuwa (mukaman majalisa) ga mutane masu zaman kan su ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kyau a ce an yi zama da kyau an tattauna, ina tunanin jam’iyya mai mulki (APC) ba tayu abin da ya kamata ba.
Babu wanda yake da wani kulli a kan zababben shugaban kasa, amma shi Tinubu bai kamata ya shigo ciki ba."
- Ifeanyi Ubah
Premium Times ta ce Mr Ubah yana ganin gaggawar Tinubu wajen yin shiga babu sharo shanu.
A cewar Sanatan na Kudancin Anambra, yankin da ya fito na Kudu maso gabas ya kamata a bar wa shugaban majalisar dattawa ba Kudu maso kudu ba.
‘Dan siyasar ya ce daga yankinsa, su na da Sanatoci a APC da za su iya jagorantar majalisar dattawa irinsu Sanata Orji Kalu Kalu ko kuwa Osita Izunaso.
An rahoto Uba ya ce zababbun Sanatocin yankinsa za su yi zama domin tsaida ‘dan takaran da za su zaba, ya kuma tabbatar da cewa zai fito ne daga kasar Ibo.
Yadda aka bullowa sha’anin rabon mukaman bai yi wa Sanatan na YPP dadi ba, yana ganin ina laifi a fara yin magana da su kafin a tsaida Godswill Akpabio.
Tikitin Yari/Kalu
Kamar dai a 2015, wasu ‘Yan majalisar za su yi bore, su kada kuri’arsu ga Orji Uzor Kalu da Abdulaziz Yari, an samu labari kawuna sun rabu a Majalisa.
Sanatoci 18 daga jihohin Arewa sun rubuta wasika zuwa ga Shugaban APC, sun ce ba su tare da Jam’iyya a kan maganar zaben Godswill Akpabio/Barau Jibrin.
Asali: Legit.ng