Lauyan Abba Gida-Gida Ya Yi Maganar Yiwuwar Samun Nasarar APC da Gawuna a Kotu
- Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wazirci yana ganin APC ba ta kama hanyar samun nasara a Kano ba
- Jam’iyya mai mulki ta kai kara a kotun zabe bayan Abba Kabir Yusuf da NNPP sun lashe zaben bana
- Barista Tudun Wazirci a matsayinsa na Lauyan NNPP ya nuna ba su shakkar rantsar da Abba Gida-Gida
Kano A wata hira ta musamman da aka yi da Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wazirci, ya nuna ba su jin dar-dar a shari’ar zaben Gwamnan jihar Kano.
Barista Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wazirci shi ne Lauyan jam’iyyar NNPP da Abba Kabir Yusuf, ya samu lokaci ya zanta da gidan rediyon Express FM.
An tambayi Lauyan game da abin da yake yawo cewa za a ruguza nasarar NNPP a zaben Gwamna, ya ce su ma su na ji ana fadan haka, kuma su na mamaki.
Masanin shari’ar yake cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayansu da ke tunanin kotun korafin zabe za ta ba Nasiru Yusuf Gawuna nasara, sun dimauce.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba haka ake shari'ar zabe ba
A cewar Lauyan, shari’ar zabe ta na da ka’idojin aiki, daga ciki sai an sanar da korafi ga wadanda ake kara, a ba shi dama ya maida martani cikin kwanaki 20.
Daga nan sai a sake ba masu kara kwanaki biyar, bayan nan ne za a bukaci a fayyace komai kafin a fara zaman sauraron hukuncin da Alkalai za su zartar.
Bashir Tudun Wazirci ya ce har yanzu NNPP ta na da ragowar fiye da kwanaki 10 ta bada martani, kafin a kai ga maganar yanke hukunci da wasu su ke yi.
Abba Kabir Yusuf bai tsoron shari'a
Tudun Wazirci ya musanya zargin sun guji karbar korafin APC, ya ce sai da kotun sauraron korafin zabe ta ba su hakuri, ya ce Abba Kabir Yusuf bai gudun shari’a.
Zuwa yanzu Lauyan na NNPP ya ce sun maida martani, kuma za su yi bayani domin kare kan su a kotu.
Duk da jita-jitar da ake yawo da ita, masanin shari’ar ya ce ba su hango abin da zai jawo kotu tayi watsi da zaben Gwamnan jihar Kano da aka yi a watan Maris ba.
APC za ta dace a kotu?
Mai kare ‘dan takaran na NNPP ya fadawa tashar rediyon cewa ba su cikin son yin magana a kan batun da ya ke kotu ba, amma ya raunata karar da APC ta shigar.
Kafin a iya biyawa mai kara bukatarsa, Lauyan na Abba Yusuf ya ce sai an yi karar kowane bangare a gaban Alkali, akasin abin da Lauyoyin APCmai-ci suka yi.
A hakura a bi Tinubu - Ogunwusi II
A babban zabe, an ji labari Sarkin Ife ya roki wadanda za ku zabi PDP da LP a 2023, su sallama su bi Bola Tinubu domin a kai Najeriya zuwa ga tudun mun-tsira.
Mai martaba Adeyeye Babatunde Enitan Ogunwusi Ojaja II ya yi wannan kira, ya ce tun da zaben shugaban kasa ya wuce, ya kamata a ajiye makaman siyasa.
Asali: Legit.ng