Abin da ya sa Arewa maso Yamma ta Samu Shugabancin Majalisar Wakilai da Dattawa a APC
- Tajuddeen Abbas shi ne wanda APC ta tsaya masa domin ya karbi shugabancin majalisar wakilai
- Mutanen Arewa maso Yamma sun fi kowa cin riba da yadda jam’iyyar APC ta yi kason kujerunta
- Yankin zai tashi da shugaban majalisar wakilan tarayya da mataimakin shugaban majalisar datttawa
Abuja - Tajuddeen Abbas wanda yake sa ran zama shugaban majalisar wakilan tarayya ya yi bayanin dalilin ba Arewa maso yamma fifiko a APC.
A hirar da ya yi a tashar Channels a ranar Lahadin da ta wuce, Honarabul Tajuddeen Abbas ya ce ba a banza ake ba Arewa maso Yamma muhimmanci ba.
Tajuddeen yankinsa ya tsira da takarar shugabancin majalisar wakilan tarayya da mataimakin shugaban majalisar dattawa ne saboda gudumuwarsa.
An yi la'akari da yawan ‘ya‘yan APC da za su tafi majalisa daga yankin, baya ga haka Iya ya ce sun ba jam’iyya mai mulki gudumuwa sosai a zaben 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yawan 'Yan Majalisa
‘Dan siyasar ya ce kusan 26% na kujerun da ake da su a majalisar wakilan tarayya, na Arewa maso yamma ne saboda haka sun zarce kowane yanki a adadi.
Premium Times ta rahoto ‘dan majalisar yana mai cewa ba don APC ta fito da tikitin Musulmi da Musulmi ba, da sun nemi shugabancin majalisar dattawa.
Dr. Tajuddeen ya ce ganin Bola Tinubu da Kashim Shettima duk Musulami ne kawai ya hana Arewa maso yamma neman kujera ta uku a matsayi a kasa.
"Arewa maso yamma na da jihohi bakwai a zaben da ya wuce, mun ba zababben shugaban kasa kuri’u fiye da miliyan 2.7.
A duk wani zabe kafin yanzu, yankin da ya fi kowane yawan kuri’u shi ne Arewa maso yamma.
Sannnan Arewa maso yamma yana da mutane 93 a cikin 360, kusan 2% na daukacin majalisa kenan, dole a duba wannan.
A cewar Abbas, babu wasu ‘yan majalisa da ba su goyon bayan yadda APC tayi kason mukamai.
Sannan Iyan na Zazzau ya yi watsi da masu zargin zai zama ‘dan amshin-shata, ya ce rashin zagin mutane da cin mutunci bai nufin za a juya shi.
Wanene Akpabio da Barau?
An samu rahoto shugabannin jam'iyyar APC sun gamsu shugabannin majalisar dattawa su fito daga Arewa maso yamma da Kudu maso kudu
Bayan an ware yankunan da za a kujerun, Jam’iyyar APC ta ayyana Godswill Akpabio da Barau Jibrin, mun kawo tarihin rayuwa da siyasarsu.
Asali: Legit.ng