Saura Kwana 20 Ya Sauka, Fashola Ya Nemawa Mutum 383,431 Aiki a Kujerar Minista
- Ganin lokacinsa ya zo karshe, Raji Babatunde Fashola ya jero alheran da ma’aikatarsa ta kawo
- Ministan ayyuka da gidajen kasar ya ce a shekaru shida, sai da su ka nemawa mutane 380, 000 aiki
- Fashola SAN ya ce Muhammadu Buhari ya kawo juyin juya hali ta fuskar abubuwan more rayuwa
Abuja - Ministan ayyuka da gidaje, Raji Babatunde Fashola (SAN) ya yi bayanin irin kokarin da ya yi a kan kujerar Minista da ya rike na tsawon lokaci.
A ranar Litinin, This Day ta ce Raji Babatunde Fashola ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo sauyi ta fuskar abubuwan more rayuwa.
Ministan tarayyar ya ce ba a taba ganin canji kamar wannan lokaci ba, a dalilin haka ne ya ce gwamnatinsu ta nemawa dinbin mutane hanyar cin abinci.
Aikin hanyoyi da aka yi
Babatunde Fashola ya ce ayyuka 383,431 aka samu daga shekarar 2016 zuwa 2022 a dalilin gina abubuwan more rayuwa, musamman ta bangaren tituna.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A tsawon lokacin da ya yi a ofis, Ministan ya ce sun yi hanyoyin kilomita 9,290.34 da zanen mita miliyan 2.2 da kuma alamu 254,690 a kan titunan tarayya.
Rahoton ya ce Ministan ayyukan ya nuna daga 2019 zuwa 2023, majalisar FEC ta amince da ayyukan yin tituna 155 da kuma wasu ayyukan gidaje 13.
Haka zalika a shekaru hudun farko na gwamnati mai-ci, Fashola ya ce an amince da ayyuka fiye da 800 a lokacin shi ne yake rike da ma’aikatar lantarki.
Abubuwan da aka yi amfani da su
Tsohon Gwamnan na jihar Legas ya yi wannan bayani ne a garin Abuja, ya na mai cewa an yi amfani da ton miliyan 3.1 na siminti wajen gina hanyoyi.
Baya ga haka akwai litoci biliyan 1.29 na man dizil da litoci miliyan 71.6 na man fetur da aka batar wajen ayyukan, baya ga dinbin bitumen da yashi da dutse.
A jawabin da ya yi, Ministan kasar ya yi bayani filla-filla a kan abubuwan da aka yi amfani da su wajen gina gadoji a hanyoyin tarayya daga 2021 zuwa yau.
Ministan ya ce an saye langa-langa 1, 374 domin gyaran gadoji da jarkoki 4,652 na fenti da tayilhar na 26,273 sqm, baya ga haka akwai kofofin karfe 1, 668.
Gwamnati mai barin-gado ta na gina gidaje fiye da 6, 000 a wurare 46 da ke jihohi da birnin tarayya. A haka mutum 97,538 su ke samun hanyar da za su ci abinci.
2023: Takara a APC
Sai yanzu ake jin labari Muhammadu Buhari ya dauko batun zaben tsaida gwanin jam’iyyar APC, ya fadi dalilin kin marawa wani 'dan takara baya a 2023.
Shugaban kasa ya bar Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da Ahmad Lawan sun goge raini, a cewarsa ba adalci ba ne ya fifita wani a kan waninsu.
Asali: Legit.ng