Za Mu Yi Amfani da Rudanin APC, Mu Tsaida Shugabannin Majalisa Inji Sauran Jam’iyyu

Za Mu Yi Amfani da Rudanin APC, Mu Tsaida Shugabannin Majalisa Inji Sauran Jam’iyyu

  • Zuwa yanzu akwai mutane fiye da 10 da suke sha’awar shugabancin majalisar wakilai a APC
  • Rashin hadin-kan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai rinjaye zai iya jawo ‘yan adawa su yi masu kafa
  • Wasu ‘yan adawa sun dunkule a wuri guda domin ganin sun samu galaba yayin da kan APC ke rabe

Abuja - Jam’iyyun hamayya da ke da wakilci a majalisar wakilan tarayya sun yi wa APC shakiyanci a kan halin da suka shiga game da zaben majalisa.

Rahoton Vanguard ya nuna ‘yan jam’iyyar adawa su na so suyi amfani da barakar da ke tsakanin ‘ya ‘yan APC, sai su tsaida shugabannin majalisar wakilai.

Akwai mutane fiye da 10 a jam’iyyar APC da suke neman takarar shugaban majalisar tarayya, jam’iyyun adawa sun ji dadin yadda kawunansu suka rabu.

Kara karanta wannan

Jerin Wasu Sanatoci da ‘Yan Majalisa 21 da Suka Fita Zakka Tsakanin 2019 da 2023

Majalisa
Wasu 'Yan majalisar wakilai Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Wadanda aka zaba a majalisa a karkashin jam’iyyar LP sun zabi Afam Ogene a matsayin jagoransu, sun nuna ba za su raba kuri’unsu a zaben bana ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan jam'iyyar LP sun hada-kai

Duk wani ‘dan LP yana tare da Hon. Ogene bayan ya samu kuri’u 21 a wani zabe na cikin gida da aka shirya domin jam’iyyar adawar ta tsaida shugabanta.

Ana tunanin Tajudeen Abbas shi ne wanda jam’iyyar APC ta ke goyon baya ya zama shugaban majalisa, amma ‘dan majalisar ya na fuskantar kalubale.

Ana rububin shiga takara a APC

Ko daga yankinsa na Arewa maso yamma, Alhassan Ado Doguwa ya shirya karawa da Dr. Tajuddeen, Rahoton ya ce hakan yana yi wa ‘yan adawa dadi.

Saura makonni biyar ayi zaben wadanda za su jagoranci majalisar kasar nan, amma har zuwa yanzu kan wakilan jam’iyyar APC ya rabu gidaje barkatai.

Kara karanta wannan

Zababbun ‘Yan Majalisa Sun Fadi Wanda Suke Goyon Baya Ya Zama Sabon Shugaba

Labari ya zo cewa Ahmed Wase, Aliyu Betara, Sada Soli da Sani Jaji sun hadu a wani gida a ranar Asabar, su ka yarda su hada-kansu domin yin aiki tare.

Abin da hakan yake nufi shi ne manyan ‘yan majalisar za su yaki takarar Tajudeen Abbas a APC.

Majiyoyi dabam-dabam sun shaidawa jaridar ‘yan majalisar nan hudu su na da kuri’u 287, abin da ya rage shi ne tsara yadda za su hada-kai a zaben bana.

Kudu maso gabas ba ta tare da Akpabio

A rahotonmu, an ji Sanatocin Ibo su na so zababben shugaban kasa watau Bola Tinubu ya yi la’akari da halin da Najeriya ta ke ciki wajen raba mukamai.

‘Yan siyasar na Kudu maso gabas ba su tare da Godswill Akpabio, sun amince su goyi bayan ‘yan takaran yankinsu da ke harin shugabancin majalisa a APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng