Baraka a Majalisa: ‘Yan Takaran Jam’iyyar APC Za Su Yi Fito na Fito da Bola Tinubu
- Da alama Hon. Tajudeen Abbas (APC, Zaria) ya samu goyon bayan Bola Tinubu a tseren majalisa ta 10
- Duk da ana tunanin zababben shugaban kasa ya nuna matsayarsa, ‘yan takara ba su da niyyar hakura
- Nasir El-Rufai da Femi Gbajabiamila ake tunanin sun tsayawa Abbas, hakan bai nufin ya yi nasara
FCT, Abuja - Alamu na nuna wasu masu neman kujerar shugaban majalisar wakilai a kasar nan za su yaki Hon. Tajudeen Abbas mai wakiltar mazabar Zaria.
Wani rahoton Daily Trust ya nuna akwai wasu ‘yan takaran da ba su gamsu da zabin Hon. Tajudeen Abbas, za su goge raini da shi a zaben majalisar tarayya.
Ana tunanin Bola Tinubu yana goyon bayan Tajudeen Abbas da Ben Kalu su rike majalisar wakilai, amma hakan bai kwantawa wasu masu takarar ba.
Da aka zanta da wani na kusa da Tinubu, ya shaidawa jaridar lissafin da jam’iyyar APC ta yi.
“An ware kujerar shugaban majalisar wakilai zuwa Kaduna kuma Abbas aka dauka, mataimakin shugaban majalisa zai tafi Kudu maso gabas, an zabi Kalu.”
- Wani jigo a APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gbaja da El-Rufai sun tsaya masa
Manyan masu marawa Abbas wanda aka fi sani da TJ baya su ne Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa zababben shugaban kasar ya na tare da ‘yan majalisar na Zaria da da kuma Bende daga Arewa ta yamma Kudu maso gabas.
Betara da Gagdi ba su fasa ba
Da aka zanta da wasu da ke goyon bayan takarar Ahmed Idris Wase, Muktar Betara Aliyu da Yusuf Adamu Gagdi, sun nuna batun da ake yi ba zai sabu ba.
Darekta Janar na yakin neman zaben Hon. Mukhtar Betara watau Dickson Tarkighir ya ce a yau ne za su ayyana takararsu a Transcorp Hilton a garin Abuja.
Goyon bayan da abokin aikinsa ya samu daga shugaban kasa mai jiran gado bai sa ‘dan majalisar na Borno ya hakura da takarar da ya sa gaba a majalisa ba.
Shi ma Yusuf Adamu Gagdi ya cigaba da fafutukar takarsa, ya ayyana manufofin da yake da shi a majalisa, hakan ya nuna bai sallamawa Abbas da Kalu ba.
Akwai wasu sauran ‘yan takaran da ke harin kujera ta hudu a kasar, sun hada, Abubakar M. Yelleman, Sada Soli, Abdulraheem Olawuyi da Aminu Jaji.
A cikin ‘yan takaran da suka fito wannan karo a jam’iyyar APC akwai mace; Mariam Odinaka Onuoha.
Takarar Godswill Akpabio
Labari ya zo cewa Kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta nesanta kan ta daga mubaya’ar da wasu da sunan kungiyoyin yankin suka yi wa Godswill Akpabio.
Alhaji Musa Sa’ido ya soki matsayar wasu kungiyoyi, ya ce babu kungiyar Arewar gaskiya da za ta so goyon bayan Sanata Akpabio, domin bai kaunar yankin.
Asali: Legit.ng