Bai Kaunar Mu: Dattawan Arewa Sun Hango Hadari a Zaman Akpabio Shugaban Majalisa

Bai Kaunar Mu: Dattawan Arewa Sun Hango Hadari a Zaman Akpabio Shugaban Majalisa

  • Wani daga cikin ‘Yan ACF, Alhaji Musa Saidu ya nuna adawarsu ga burin Godswill Akpabio a majalisa
  • Hakan na zuwa ne bayan an ji wasu ‘Yan Arewa su na goyon bayan Akpabio ya rike majalisar dattawa
  • Saidu ya ce Kungiyar Dattawan Arewa ba ta tare da wasu domin Sanatan ba masoyin Arewa ba ne

Kaduna - Kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta nesanta kan ta daga mubaya’ar da wasu da sunan kungiyoyin yankinta suka yi wa Sanata Godswill Akpabio.

A rahoton da aka samu daga Daily Trust, wata kungiya ta gamayyan mutanen Arewa ta na goyon bayan Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa.

Wani jawabi da Alhaji Musa Saidu ya fitar a ranar Lahadi, ya nuna kungiyarsa ta ACF ba ta da wani hadi ta kusa ko ta nesa da tsohon Gwamnan na Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Baraka a Majalisa: ‘Yan Takaran Jam’iyyar APC Za Su Yi Fito na Fito da Bola Tinubu

A matsayinsa na jagoran mutanen Arewa a Kudancin Najeriya, Musa Saidu ya ce yin mubaya’a ga Akpabio a zaben majalisa, zai jefa 'Yan Arewa a cikin masifa.

Godswill Akpabio
Sanata Godswill Akpabio a Majalisa Hoto: newsdigest.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba mu tare da CNG" - ACF

"Mu na masu nesanta kan mu daga mubaya’ar da gamayyar kungiyoyin Arewa suka yi wa Sanata Godswill Akpabio a zaben majalisar dattawa.
Ba da yawun Arewa gamayyar ta ke magana ba, ta na magana ne da yawun kan ta. Babu kungiyar Arewar gaskiya da za ta so goyon bayan Akpabio a kujera mai muhimmanci irin shugaban majalisa dattawa saboda bai kaunar yankin Arewa.
Mu ne mutanen da mu ka san wanene Akpabio domin mu ne mazauna Kudu, mun san masu kaunar mutanen Arewa, kuma Akpabio bai cikinsu.

Alhaji Musa Saidu

Jahilci ko kudi?

A cewar Saidu, watakila rashin sani ya jawo kungiyar tayi kuskuren goyon bayan zababben Sanatan.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Tinubu Ya Ayyana Wadanda Yake So, Yari Ya Ce Zababben Shugaban Kasar Ya Yi Kadan

A jawabinsa, VON ta rahoto shi yana mai Allah-wadai da mubaya’ar, ya kara da cewa babu mamaki an yi amfani da kudi wajen sayen kungiyoyin yankin.

Duk da ba da yawun ACF yake magana ba, amma a matsayinsa ya nuna babu dalilin da za a ce dole sai daga Kudu ne shugaban majalisar dattawa zai fito.

Rashin 'Yar'adua - Turai

A wata hira da aka yi da ita, an ji labari Hajiya Turai ‘Yar’adua ta ce tun da Umaru Musa ‘Yar’adua ya kwanta ciwo, ta ke azumi har ya rasu a Mayun 2010.

Turai mai shekara 65 ta ce saboda mijinta yana kaunar ta ne aka rika jifar da suka iri-iri, ta fadawa Remi Tinubu ta shirya zama mai hakuri a fadar Aso Villa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng