Mataimakiyar Gwamna Ta Farko A Najeriya Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Barin Najeriya Saboda Tinubu

Mataimakiyar Gwamna Ta Farko A Najeriya Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Barin Najeriya Saboda Tinubu

  • A hirar ta da manema labarai, Sinatu Ojikutu ta janye kalaman da ta yi a baya na cewar za ta yi hijira daga Najeriya muddun Tinubu ya ci zaɓe
  • Ta ce koyarwar addinin ta na Musulunci ne ya sa ta janye kalaman da ta yi a baya
  • Ojikutu ta ce ba za ta iya ƙyale Najeriya ba amma za ta ci gaba da yin magana idan ta ga ana cusguna ma 'yan ƙasa

Mace ta farko da ta fara zama mataimakiyar gwamna a Najeriya, Hajiya Sinatu Ojikutu ta ce ta janye batun da ta yi a baya na cewar za ta bar Najeriya idan Tinubu ya ci, wanda yanzu haka ake shirin rantsarwa a ranar 29 ga wannan watan na Mayu da muke ciki.

Ojikutu wacce ta yi ma tsohon gwamnan jihar Legas Gwamna Michael Otedola mataimakiya ta yi aman ta lashe duk da iƙirarin da ta yi ta nanatawa wasu satika baya da suka wuce kan cewar za ta bar Najeriya ta tafi wata ƙasar ta yi rayuwarta Legit ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Turai ‘Yar’adua Ta Tuna da Lokacin Karshe da Marigayi Shugaba ‘Yar’adua a Aso Rock

Ojikutu
Mataimakiyar Gwamna Ta Farko A Najeriya Hajiya Sinatu Ojikutu. Hoto: Guardian
Asali: UGC

Hijirar ta saba da koyarwar addinin Musulunci

A wata tattaunawa da ta yi da jaridar Punch, Ojikutu ta ce yin hijira daga ƙasar ta ta haihuwa ya saɓa ma koyarwar addinin Musulunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka tambaye ta kan ko ta janye kalaman da ta yi kan alwashin da ta shi na yanke alaƙar ta da Najeriya sai ta kada baki ta ce:

“Yanke alaƙa ta da Najeriya a yanzu ka iya zama wata matsalar ta daban saboda wani malamin addinin Muslunci ya shaida min cewa ban fahimci Ƙur'ani ba ne. Ya tambaye ni ko Manzon Allah (SAW) ya yanke alaƙar shi da garin Makkah duk da barazana da rayuwar shi da aka yi mishi.”
“A sabili da haka ba zan iya ƙyale Najeriya ba. Ya ƙara da cewa ko da ma ina so inyi hijira to dole akwai wasu dalilai da za su sanya in yi hakan.”

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

Mutane da dama ne su ka fahimtar da ni

Ojikutu ta kuma ƙara da cewar akwai mutane da dama da ta ke jin nauyi da su ka same ta kan maganar barin ƙasar. Ta ce sun matsa ma ta kan tabbatar da cewa da haƙura da batun barin ƙasar.

Ta ce 'yan uwanta al'ummar musulmai da ta ke tare da su sun same ta inda suka kwaɓe akan ta daina maganganun da ta ke yi. Sai dai ita kuma ta ce ta shaida musu cewa ita fa babu wani abu da ta yi ma Tinubu da har za a ce ko ya kai inda za a iya yi mata barazana da rayuwar ta. A sabili da haka ta haƙura da tafiyar.

Kotu ta tura Ekweremadu zuwa gidan maza

A wani labarin na daban kuma, wata kotu da ke zaman ta a birnin London na ƙasar Birtaniya ta yanke ma tsohon mataimakin kakakin majalissar dattawa na Najeriya Ike Ekweremadu hukuncin ɗaurin shekaru kusan goma a gidan yari.

Kara karanta wannan

Najeriya Ta Fi Kowace Ƙasa Arhar Wutar Lantarki A Duniya, FG

Kotun ta tuhumi Ekweremadu da laifin safarar sassan jikin ɗan Adam wanda ya yi hakan domin a ciri ƙoda jikin wani matashi domin a sanya ma ɗiyar Sonia da ta ke fama da ciwon ƙoda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng