Kotun Birtaniya Ta Yanke Wa Ekweremadu Shekaru 10 A Gidan Yari Kan Safarar Sassan Jikin Bil Adama

Kotun Birtaniya Ta Yanke Wa Ekweremadu Shekaru 10 A Gidan Yari Kan Safarar Sassan Jikin Bil Adama

  • An samu Ike Ekweremadu, matar shi Beatrice da kuma likita da karya dokar nau'in ta zamani saboda yinƙurin yin amfani da ƙodar matashin
  • A hukuncin da kotun ta 'Old Bailey' ta yanke ran Juma'a 5 ga watan Mayu, ta yanke ma tsohon Sanatan ɗaurin shekaru tara da wata takwas
  • Kotun ta yanke ma matar Ekweremadu wato Beatrice hukuncin shekaru huɗu da wata shida, a yayin da shi kuma likitan aka yanke mi shi shekaru 10 a gidan kaso

Wata kotu da ke zamanta a London ta yanke ma tsohon mataimakin kakakin majalisar dattawa Ike Ekweremadu hukuncin shekaru 9 da watanni takwas a gidan yari bisa laifin safarar sassan jikin ɗan Adam, BBC Pidgin ta rahoto.

Kotun ta kuma yanke ma matar shi Beatrice hukuncin shekaru huɗu da wata shida a gidan kaso. Haka nan ma likitan Dakta Obinna Obeta wanda ya shiga tsakani, an yanke mishi hukuncin shekara goma, sannan kuma an karɓe lasisin aikin shi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Fitacciyar Kasuwa Ta Ƙasa da Ƙasa a Najeriya Ta Kama da Wuta

Ekweremadu
Ike Ekwerenadu, Beatrice, Obinna. Hoto: Punch
Asali: UGC

Akan wane laifi ake tuhumar Ekweremadu

A rahoton da majiyar Legit ta wallafa cewa ana tuhumar Ekweremadu ne dai da laifin safarar wani yaro mai kimanin shekaru 21 zuwa London da zummar a cire ƙodar shi domin sanya ma yarinyar Ekweremadu wato Sonia da ba ta da lafiya. Sai dai hakan ya saɓa ma doka domin kuwa ya na a cikin abubuwan da su ka shafin nau'in bauta ta zamani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masu tuhumar sun ce an yi ma likitocin asibitin ƙaryar cewa yaron wai ɗan uwan Sonia ɗin ne duk don a gamsar da su domin su yi ma ta aikin dashen ƙodar akan zunzurutun kuɗi har fam dubu tamanin (£80,000) a asibitin 'The Royal Free' da ke a birnin London.

Ekweremadu ya yi ma matashin alƙawarin kuɗaɗe masu yawa

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

An ce an bawa matashin wasu maƙudan kuɗaɗen da suka saɓa ƙa'ida domin ya ba wa Sonia ƙoda wacce ta ke fama da cutar ƙoda da ta yi sanadin dakatar da karatun digiri na biyu da ta ke yi a ɓangaren wasan kwaikwayo a Jami'ar Newcastle.

Jam'in da ke shigar da ƙara ya ce Ekweremadu da matar shi sun ba wa matashin Fam dubu bakwai, sannan kuma su ka yi mishi alƙawarin samun damarmaki masu yawa a Birtaniya. Sai dai a lokacin da su ka je asibitin ne ya fahimci abinda ake shirin yi.

A watan Maris ɗin shekarar 2022 ne dai aka gurfanar da Ike Ekweremadu tare da matar shi Beatrice bisa tuhumar su da ake yi da ƙoƙarin yin safarar ƙodar matashin ɗan shekara 21. Ekweremadu ya yi hakan ne a ƙoƙarin ceto rayuwar ɗiyar shi Sonia da ke fama da ciwon ƙoda.

Ekweremadu ya yi iya bakin ƙoƙarin shi wajen ganin cewa ya samu sassauci a hukuncin da kotun za ta yanke mishi shi da matar ta shi. Sannan mutane da ma wasu hukumomin da dama sun sanya baki wajen ganin an yi ma Ekweremadu sassauci a hukuncin. Sai dai hukuncin kotun na ranar juma'an nan na nuni da cewa koken na shi bai samu karɓuwa ba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankalin Da Muka Shiga a Sudan Ba Ɗan Kaɗan Ba Ne, In Ji Ɗalibi Bello Halliru

Ba na fatan Najeriya ta faɗa halin tarzoma irin na Sudan

A wani labarin na daban kuma, kun ji yadda wani ɗalibi da ya ke karatun likitanci a Sudan ya bayyana irin halin da su ka shiga a sakamakon rikicin da ya ke faruwa a ƙasar ta Sudan.

Ɗalibin wanda ya na cikin mutane 374 da aka samu damar kwasowa daga ƙasar ta Sudan a ranar Laraba, ya shaida ma manema labarai cewar ba ya fatan wani ya fuskanci irin bala'in da suka fuskanta. Sannan ya ƙara da cewar ya na fatan Najeriya za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta kauce ma faɗawa cikin tarzoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel