Majalisar Tarayya Ta 10: Umahi Ya Janyewa Akpabio Wajen Neman Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa
- Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya janye daga tseren kujerar shugaban majalisar dattawa sannan ya marawa takwaransa Godswill Akpabio baya
- A cewar Gwamna Umahi, zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya nemi ya janye
- Sai dai, ya bayyana cewa ba zai shiga tseren kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa ba
Abuja - Wani sabon ci gaba a majalisar dokokin tarayya ya tabbatar da cewar zababben Sanata kuma gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya janye daga kudirinsa na son zama shugaban majalisar dattawa.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Gwamna Umahi ya janye kudirin nasa ne domin marawa takarar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio baya.
Gwamna Umahi ya bayyana cewa ya gana da zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda ya umurce shi da kada ya yi takarar kujerar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu, jim kadan bayan ganawa da Tinubu, yana mai cewa ba zai kasance a cikin masu neman kujerar mataimakin shugaban majalisar ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Umahi ya ce:
"Dan uwana (Akpabio) ya zo ya tuntube ni.
"Jiya, na ga zababben shugaban kasa bisa gayyatarsa kuma ya fada mani cewa ya rigada ya jajirce, kuma cewa 'dan Allah kada ka yi takara' kuma na amince sannan na janyewa dan uwana, Sanata Akpabio.
"Shine dan takarar hadin gwiwata. Kuma na janye masa a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa."
Sanata mai wakiltan Borno ta kudu, Ali Ndume ya fada ma manema labarai cewa Akpabio ne dan takarar da aka tsayar.
Sai dai kuma, Sanata Ndume bai fito fili ya bayyana ko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ko da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu yake ba.
“Za Su Kashe Ni”: Matashin Da Aka Yi Safarar Sassan Jikinsa Ya Roki Gwamnatin Birtaniya Ta Ba Shi Mafaka
Ya ce:
"Kamar yadda kuke gani, ina jagorantar kamfen din Akpabio saboda shine dan takarar da shugaban kasa ya fi so kuma mun sanya ra'ayin kasar da na jam'iyya sama da na kowa."
Matsayin Sanata Ndume ya kuma yi daidai da na Gwamna Abdullahi Ganduje na cewa Akpabio ne ya dace da kujerar shugaban majalisar dattawan.
Dangantakar Wike da Tinubu ba za ta je ko'ina ba, Malamin addini ya yi hasashe
A wani labarin kuma, wani babban faston Najeriya, Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa za a tashi baran-baran tsakanin Gwamna Nyesom Wike da Gwamnatin Bola Tinubu saboda APC za ta ci amanarsa kamar yadda ya ci na jam'iyyarsa ta PDP.
Asali: Legit.ng