Kamar Buhari, Bola Tinubu Ya Sha Alwashin Yaki da Rashin Gaskiya a Mulkinsa
- Idan Asiwaju Bola Tinubu ya karbi ragamar shugabancin Najeriya, zai yaki marasa gaskiya a kotu
- Gwamnati mai zuwa za ta maida hankali a kan jin dadin ma’aikatan shari’a domin a daina barna
- Da ya bude wasu kotu da aka gina a Ribas, Tinubu ya sha alwashin zai tafi da kowa a gwamnati
Rivers - Asiwaju Bola Tinubu, ya yi alkawari gwamnatinsa za tayi kokari wajen ganin ma’aikatan shari’a sun daina sha’awar rashin gaskiya.
The Cable ta ce zababben shugaban Najeriyan ya yi wannan bayani a wajen bude wasu kotun majistare da gwamnatin Ribas ta gina a Fatakwal.
Da yake magana ranar Alhamis a jihar Ribas, Abdulaziz Abdulaziz ya rahoto shugaban mai jiran gado yana cewa zai yaki rashin gaskiya a kotuna.
Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta kawo sauye-sauyen da suka dace domin magance matsalar rashin gaskiya daga bangaren shari’a a Najeriya.
Idan bera na da sata, daddawa na da wari
"Bai yiwuwa Alkalanku su zauna a cikin talauci, su yi aiki a wulakance, sannan su yi adalci a irin halin da suke ciki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wannan yana cikin sauye-sauyen da ake bukata. Dole mu yaki barna, amma kuma dole mu duba wani bangaren.
Idan ba a so Alkalai su yi rashin gaskiya, dole a maida hankali ga walwalarsu. Ba za su yi aiki a yanayi mai hadari ba."
- Bola Tinubu
Abdulaziz Abdulaziz yake cewa Bola Tinubu ya yi alkawari zai dage wajen rage sha’awar barna daga wajen wadanda suke zartar da shari’a a kotu.
Alkawarin da tsohon gwamnan na legas ya yi shi ne zai duba tsare-tsaren shari’a a Najeriya. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto a yau.
Tinubu zai tafi da kowa
Bayan cewa gwamnatinsa za tayi wa kowa adalci, an rahoto Tinubu ya kara da cewa zai yi ayyukan da za su a rika tunawa da shi a ko ina a kasar nan.
A ra’ayin Tinubu, ma’aikata su na aukawa rashin gaskiya ne idan su ka rasa hanyoyin mallakar abubuwan jin dadin rayuwa irinsu gidaje da motoci.
Abdullahi Ganduje a Kalaba
Da ya ziyarci garin Kalaba a jihar Kuros Riba, an ji labari Abdullahi Umar Ganduje ya fadi wanda Gwamnonin APC suke goyon baya a zaben majalisa.
Abdullahi Ganduje ya ce Shugaban majalisa zai fito daga Kudu maso kudu, ba kowa ne wannan ba illa tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio.
Asali: Legit.ng