Ana Dab Da Rantsar Da Shi, Bola Tinubu Ya Sha Wani Muhimmin Alwashi
- Yana dab da ya hau kan karagar mulkin ƙasar nan, Bola Tinubu ya sha wani muhimmin alwashi
- Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya sha alwashin cewa zai cika dukkanin alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe
- Tinubu ya sha wannan alwashin ne lokacin da ya ke ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar Rivers
Jihar Rivers - Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin cika dukkanin alƙawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe, idan ya hau kan ragamar mulkin ƙasar nan a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Jaridar Punch tace Bola Tinubu ya sha wannan alwashin ne ranar Alhamis, a birnin Port Harcourt na jihar Rivers, lokacin da ya ke ƙaddamar da ginin harabar kotun majistare, wacce gwamna Nyesom Wike, ya gina.
A kalamansa:
"Gyara yana nan tafe, ina nan a tare da ku da fatan cewa za ku haɗa hannu da ni, na yi mu ku alƙawarin jajircewata wajen ganin na cika dukkanin alƙawuran da na ɗauka."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Na yi wa ƴan Najeriya alƙawarin cewa haɗin kan ƙasar nan babu tantama a kansa. Wannan shine abinda ni da gwamna Wike mu ke tallatawa tare. Na yi alƙwarin zan yi wa kowa adalci."
Tinubu ya yabawa gwamna Wike kan gina harabar kotun, wanda ya bayyana matsayin mai kyau, inda ya yi nuni da cewa babu wata hanyar da ta fi dacewa a yaƙi cin hanci a ɓangaren shari'a, fiye da kula alƙalai da tabbatar da cewa suna cikin walwala.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya bayyana cewa, a hakan gwamna Wike yaƙar cin hanci ya ke da rashawa, cewar rahoton Leadership.
"Na kalli abinda gwamna Wike ya yi yau ta wata fuska. Wannan yaƙar cin hanci da rashawa ne, sannan ka bayar da gudunmawar ka sosai ta wannan fannin." A cewar Tinubu
Lauyoyi 50 Za Su Kare Nasarar Bola Tinubu a Kotu
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa Bola Tinubu, ya haɗa wasu manya-manyan lauyoyi da za su kare nasarar sa a kotu.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya zaɓo manyan lauyoyi 50 da ake ji da su, domin kare nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa a gaban kotu.
Asali: Legit.ng