Jerin Wasu Sanatoci da ‘Yan Majalisa 21 da Suka Fita Zakka Tsakanin 2019 da 2023

Jerin Wasu Sanatoci da ‘Yan Majalisa 21 da Suka Fita Zakka Tsakanin 2019 da 2023

  • Nan da ‘yan kwanaki kadan majalisa ta tara za ta shude, za a rantsar da sabuwar majalisar tarayya
  • A majalisa mai-ci, an samu wasu ‘yan siyasa da suka yi fice, su ka yi wakilcin da za a rika tuna su
  • Ayyukan ‘yan majalisa sun hada da sa-ido, kirkiro ayyuka, inganta rayuwar jama’a da wakilci

Abuja - A wani rahoto da aka samu a The Nation, an tattaro ‘yan majalisar wakilan tarayya da na dattawa da wakilcinsu ya yi tasiri daga 2019 zuwa 2023.

1. Hon. Olubunmi Tunji-Ojo

A majalisa ta tara, za a rika tunawa da Hon. Olubunmi Tunji-Ojo mai wakiltar Akoko ganin yadda ya dage wajen binciken hukumar NDDC tare da kawowa mazabarsa ayyuka.

2. Hon. Ade Adeogun

Wani wanda ya kawo kudirori a majalisa shi ne Ade Adeogun, ‘dan majalisar ya bada gudumuwa domin ganin gwamnati ta samar da ayyukan more rayuwa ga mutanensa.

Kara karanta wannan

Zababbun ‘Yan Majalisa Sun Fadi Wanda Suke Goyon Baya Ya Zama Sabon Shugaba

3. Hon. Garba Datti Muhammad

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan majalisar Sabon Gari a Kaduna, Garba Datti Muhammad ya yi kokari wajen yi wa mazabarsa ayyuka tare da kawo ayyukan cigaba da kuma nemawa matasa ayyukan yi.

4. Hon. Mayowa Akinfolarin

Mutanen Ileoluji Okeigbo/Odigbo sun ga wakilci a wajen Mayowa Akinfolarin. ‘Dan majalisar ya yi suna a majalisar nan bayan ya kawo kudirin kafa wani asusu na NYSC.

5. Hon. Abbass Tajudeen

Ana maganar Abbass Tajudeen yana da kudiri 74 a majalisar tarayya. Watakila hakan ya sa wasu suke ganin dacewarsa ya zama shugaban majalisa ta goma da za a rantsar.

6. Hon. Babajimi Benson

Wani kwararren ‘dan siyasa kuma wanda ya dade a majalisa shi ne Babajimi Benson. Mutanen Ikorodu da kuma sojojin Najeriya za su dade ba su manta da Hon. Benson ba.

7. Hon. Mukhtar Aliyu Betara

Kara karanta wannan

DCD Ta Gano Makarkashiyar da Ahmad Lawan Suke Shiryawa Kafin Zaben Majalisa

Mazabar Biu, Bayo, Kwaya Kusara da Shani ta samu wakilci mai kyau a wajen Mukhtar Aliyu Betara. ‘Dan siyasar ya jagoranci kwamitin kasafin kudi ba tare da badakala ba.

8. Hon. Alhassan Ado Doguwa

Idan ana maganar majalisa ta tara, dole a kawo sunan Alhassan Ado Doguwa tun daga lokacin da ya sake lashe zaben T/Wada da Doguwa, ya tattaro matansa zuwa zauren majalisa.

9. Hon. Abubakar Kusada

Wani ‘dan majalisa da har mutanen wasu jihohi suke yaba masa shi ne Abubakar Yahaya Kusada, duk da irin taimakon da ya yi wa al’ummar Kankiya/Kusad/Ingawa, ba zai zarce ba.

10. Hon. Abubakar Kabir Abubakar

Daga zuwansa majalisa a APC, aka dauki kwamitin ayyuka aka damkawa Abubakar Kabir Abubakar. A kullum mutanen yankin Bichi murna suke yi da samun wakilcinsa.

Majalisar wakilai
Femi Gbajabiamila a Majalisar wakilai Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

11. Hon. Zainab Gimba

A shekarar 2020 Zainab Gimba tayi abin da ya ba kowa mamaki, ‘yar majalisar ta rabawa mutanen Bama, Ngala da Kala Balge motoci, keke napep da kekunan dinki na makudan kudi.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun Adawa Sun Yi Taro, An Tsara Yadda Za a Yaki ‘Yan Takaran APC a Majalisa

12. Muhammad Gudaji Kazaure

Muhammed Kazaure Gudaji mai wakiltar Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi bai lafa a majalisa ta tara ba musamman da ya zargi Gwamnan bankin CBN da badakalar makudan kudi.

13. Sanata Tolu Odebiyi

Sanatan jihar Ogun ya tamma Tolu Odebiyi ya yi abin a yaba, a shekaru hudun nan da ya shafe, mutanen mazabarsa za su dade ba su manta da irin wakilcin da ya yi masu.

14. Sanata Sani Musa

Sanatan Neja ta gabas, Sani Musa ya kawo kudirori fiye da 15 da za su taimaki kasa ta bangaren kiwon lafiya, yakar masu sharri a yanar gizo da wadanda aka yi wa fyade.

15. Sanata Abba Moro

Sabon Sanatan kudancin Benuwai, Abba Moro ya kawo kudirori 12 da korafi biyar a a shekaru hudu, tsohon Ministan cikin gidan ya ba majalisar dattawa gudumuwa sosai.

16. Solomon Olamilekan Adeola

Bayan ya zarce a matsayin Sanata mai wakiltar Yammacin Legas, Solomon Olamilekan Adeola ya yi amfani da damar musamman wajen taimakawa jiharsa da yankin da ya fito.

Kara karanta wannan

Kujerar Kakaki: Ado Doguwa Ya Ce Mata 4 Da 'Ya'ya 28 Yake Dashi, Zai Iya Ji da Majalisa

17. Sanata Muhammad Adamu Aliero

Wani Sanatan da aka yaba da shi a rubutun nan shi ne na Kebbi ta tsakiya, Muhammad Adamu Aliero ya taka rawar gani, babu mamaki hakan ya ba tsohon Ministan damar zarcewa a PDP.

18. Sanata Elisha Abbo

Elisha Abbo yana cikin masu mafi karancin shekaru da suka taba zama Sanata a tarihi. ‘Dan majalisar bai kauracewa mutanen Adamawa ta Arewa ba, da su aka ci majalisa ta tara.

19. Barau Jibril

Ba ayi mamaki da Sanatan Arewacin Kano watau Barau Jibril ya tsallake guguwar NNPP a Kano ba, Jibril ya rike kwamitin kasafin kudi kuma ya kawo cigaba sosai ga ‘yan mazabarsa.

20. Sanata Orji Uzor Kalu

Orji Uzor Kalu ya taka rawar gani a majalisa wajen yaki da zaman kashe wando a matsayin shugaban masu tsawatarwa, Sanatan na Arewacin Abia ya yi zaman gidan yari.

21. Sanata Uba Sani

An dade ba a samu wanda ya yi wakilci irin na Sanatan Kaduna majalisa ba. Uba Sani ya bada gudumuwa bila-adadin, shi kadai Sanatan da ya lashe zaben Gwamna a 2023.

Kara karanta wannan

‘Dan Majalisar Kano da Ake Zargi da Kisan Kai Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa

Takarar Mukhtar Aliyu Betara

Hon. Mukhtar Aliyu Betara yana da goyon bayan dinbin mutane a zaben majalisar tarayya, rahoto ya ce mutane daga jam’iyyu dabam-dabam su na tare da shi.

‘Dan majalisar na Biu/Kwayar/Kusar/Bayo/Shani ya karyata zargin da aka yi masa na yakar jam’iyya, zai iya bata lissafin da APC za ta yi a wajen kason kujeru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng