Shehu Sani ya Bada Muhimman Shawarwari 4 da Za su Iya Taimakon Bola Tinubu a Mulki
- A cikin hikimar da ya saba, Shehu Sani ya bada wasu shawarwari ga wadanda za su karbi mulki
- Tsohon ‘dan majalisar kasar ya yi wani gajeren rubutu a dandalin Facebook mai daukar hankali
- Sanata Shehu Sani ya ankarar da shugabanni masu jiran gado a kan yadda za su kula da fadarsu
Abuja - Shehu Sani ‘dan siyasa ne wanda kuma ya yi suna wajen gwagwarmaya a Najeriya, ya kan tofa albarkacin baki a kan sha’anin kasa.
Yayin da ake shirin karbar mulki, an ji fitaccen ‘Dan siyasar ya yi wasu maganganu na azanci a shafinsa na Facebook a matsayin shawarwari.
Kwamred bai kama suna ko mukamin wadanda yake ba shawara ba, amma ya nuna cewa kira ne ga wadanda za su rike madafan iko a Abuja.
Sanata Sani Shehu ya bada shawarar ne a bulus, ma’ana kyauta ba tare da an tambaye shi ba.
Sai an yi hattara a mulki
Daga cikin abin da wannan shawara ta kunsa shi ne wanda zai dare kujerar mulki ya yi hattara da makiya da kuma na-kusa da masu barin ofis.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Haka zalika tsohon Sanatan na Kaduna ya ankarar da wadanda za su karbi shugabanci a kan wasu boyayyu da ke rike da madafun iko.
Kamar yadda ya rubuta a Facebook, Sanata Sani ya nuna akwai wadanda ba don Allah za su shigo fadar mai mulki ba, ya doke ‘dan takaransu ne.
Idan kunne ya ji...jiki ya tsira
"Shawara a bulus ga sabon mai mulki da za ayi a Abuja:
Ka da ka gaji na-hannun daman shugaba mai barin gado, kai ma za su ci amanarka.
Ka da ka gaji makiyan shugaba mai barin gado, kai ma za su yake ka.
Ka da ka gaji masu juya akalar gwamnatin shugaba mai barin gado, kai ma za su juya ka.
Ka sa ido a kan wadanda suka shigo fadarka alhali ba kai ne asalin zabinsu na farko ba.
Ka fi maida hankali a game da abin da suka fada da harshensu, ba da Ingilishi ba."
- Shehu Sani
HYPREP ya yi sabon shugaba
A ranar Larabar nan ne rahoto ya zo cewa fadar shugaban Najeriya ta bada sanarwa cewa an yi waje da wanda yake jagorantar aikin HYPREP.
An sanar a Twitter cewa Farfesa Nanibarini Zabbey zai dare kujerar shugaban HYPREP ba tare da bata lokaci ba, ya canji Dr. Ferdinand Giadom
Asali: Legit.ng