‘Yan APC Sun Hada-Kai da PDP, LP da NNPP, Sun Yi Taron Dangi a Majalisar Tarayya
- Wasu ‘Ya ‘yan APC sun hada-kai da jam’iyyun adawa wajen kafa wata kungiya a Majalisar tarayya
- ‘Yan adawan sun nuna za su kyale shugaban majalisar wakilai ya fito daga jam’iyya mai rinjaye
- Bello Kumo da Kingsley Chinda aka zaba a matsayin shugabannin tafiyar, NNPP ta tashi da Sakatare
Abuja - Zababbun ‘yan majalisar tarayya daga jam’iyyun siyasa takwas da za a rantsar a 2023 sun nuna za su goyi bayan matakin da APC za ta dauka.
Premium Times ta ce ‘Yan adawan na majalisa da wasu ‘ya ‘yan APC ba za su bijirewa jam’iyyar APC a kan batun yankin da za a fito da shugabanni ba.
‘Yan majalisar sun yi wannan bayani yayin kaddamar da wata kungiya ta hadin gwiwa a Abuja.
An zakulo ‘ya ‘yan kungiyar ne daga jam’iyyun APC, PDP, LP, NNPP, APGA, ADC da YPP, amma ba kowane ‘dan jam’iyya ne a cikin kungiyar hadakar ba.
Yadda APC ta dama, haka za a sha
Shugaban wannan tafiya, Hon. Bello Kumo (APC, Gombe) ya ce ba su da wani ‘dan takara tukuna, amma su na jiran yadda APC za tayi kason mukamai ne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Rahoton ya ce Hon. Bello Kumo ya nuna a shirye suke su yi aiki da bangaren zartarwa, amma ba za su manta da gashin kai da doka ta ba majalisa ba.
Babu 'Yan a-bi yarima a sha kida
Hon. Aliyu Sani Madaki (NNPP, Kano) ya shaida cewa ba za su zama ‘yan amshin shata a majalisa ba, duk da za su ba APC damar tsaida shugabanni.
Aliyu Sani Madaki wanda zai wakilci mazabar Dala ta jihar Kano ya ce a matsayinsu na ‘yan jam’iyyun hamayya, abin da za su yi shi ne adawa na gari.
A yayin da aka zabi Kumo da Hon. Kingsley Chinda (PDP, Ribas) a matsayin shugabannin kungiyar, Madaki daga jam’iyyar NNPP ne Sakatarensu.
Sakataren kudi shi ne, Olubunmi Tunji-Ojo (APC, Ondo), sauran masu mukamai sun kunshi; Babajimi Benson (APC, Lagos) da Dennis Idahosa (APC, Edo).
Duk da APC ta na da rinjaye, amma idan aka hada ‘yan adawa a wuri guda, su na da mutane 183.
Shari'ar zaben 2023
Rahoto ya zo cewa a mako mai zuwa Bola Tinubu zai fara sanin ko zai hau kujerar shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a kotun korafin zabe.
Lauyoyin Atiku Abubakar da Peter Obi sun sha alwashin hana Jam’iyyar APC zarcewa a mulki, amma APC ta ce ba ta haufin Tinubu zai shiga ofis.
Asali: Legit.ng