Tinubu Zai San Makomar Zaben da Ya Lashe, Kotu Za Ta Fara Hukunci kan Nasarar APC
- Daga ranar Litinin za a fara zama domin yanke hukunci a kan karar zaben shugaban Najeriya
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa Kotun korafin zaben shugaban kasa na 2023 ya gaba karbar kararraki
- Abin da ya rage shi ne a zartar da hukunci bayan an saurari Lauyoyin jam’iyyun PDP, LP, AA da PDM
Abuja - Kotun da ke sauraron korafin zaben shugaban kasa ya tsaida Litinin a matsayin ranar da za a karbi karar da aka shigar a kan Bola Tinubu da APC.
A rahoton Punch na makon nan, an fahimci daga ranar 8 ga watan Mayu, za a fara shari’a inda jam’iyyun adawa ke rokon a soke nasarar da Bola Tinubu ya samu.
Mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkar shari’a, Ahmad El-Marzuq ya sanar da manema labarai a mako mai zuwa za a fara sauraron kara zuwa karshen wata.
Ahmad El-Marzuq ya nuna APC ta shiryawa shari'ar, za ta kare nasarar da ta samu a gaban kotun zabe. Lauyan Tinubu, Tayo Oyetibo SAN ya tabbatar da lamari nan.
Karbar korafi ya kare
Bincike ya nuna daga ranar 23 ga watan Afrilu, kotun ya daina karbar martanin korafi a kan zaben.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Joe-Kyari Gadzama, SAN ya jagoranci Lauyoyi su na masu neman kotu ta hana a rantsar da zababben shugaban kasa bisa ikirarin ba shi ne ya lashe zabe ba.
LP, AA, APM su na kotu
Shi ma Peter Obi wanda ya zo na uku ya ce tun wajen dauko abokin takararsa watau Kashim Shettima, wanda ake cewa ya ci zaben shugaban kasar ya saba doka.
Lauyoyin Obi da ya yi takara a LP sun ce ba jam’iyyar APC ta fi yawan kuri’u ba, sannan ‘dan takaranta a 2023 bai iya samun ko da 25% na kuri’un birnin Abuja ba.
Haka zalika wani bangare na jam’iyyar AA ta shigar da kara saboda INEC ta ki daura sunan ‘dan takararta, Solomon-David Okanigbuan a kan shafin yanar gizo a zabe.
Ita kuma jam’iyyar APM ta ce tun farko idan ana bin doka, Tinubu bai cancanci ya shiga takara ba.
A karkashin jagorancin Wole Olanipekun, SAN, Lauyoyin da suke kare jam’iyya mai ci sun bukaci ayi watsi da karar da ‘yan adawa su ka shigar a kan zaben na bana.
Kowa yana hangen nasara
Olanipekun ya ce ba yau Atiku ya fara shan kashi a takara ba, an yi haka a 2007, 2011 da 2019. Amma Mike Ozekhome ya ce su na sa ran PDP za ta yi nasara a kotu.
A baya labari ya zo cewa an yi shari’a tsakanin hukumar DSS da wasu ‘Yan PDP da ake zargi da barazanar lahanta jami’an tsaro a lokacin zaen jihar Adamawa.
A karshe, Alkalin Kotun Jiha mai zama a garin Yola ya ce wajibi ne a gaggauta fito da magoya bayan Jam’iyyar adawar da aka tsare tun a ranar 16 ga watan Afrilu.
Asali: Legit.ng