'Yan Arewa Sun Magantu: Yari Ne Kadai Ya Dace da Shugabancin Majalisar Dattawa
- Kungiyar siyasa a arewa maso yammacin Najeriya ta nemi zababben shugaban kasa da ya bai wa Abdulazizi Yari shugabancin Majalisar Dattawa
- Ta kara da cewa rashin adalci ne karara a bai wa dan wani yanki wannan kujerar matukar ba dan arewa maso yamma bane
- Kungiyar tace yankin yafi bai wa Tinubu kuri'u a zaben bana, sun bashi fiye da kashi 30 a zaben na bana
Kaduna - Wata kungiyar siyasa a Arewacin Najeriya ta amince da ba tsohon gwamnan Zamfara, Andulaziz Yaro goyon baya a matsayin shugaban majalisar dattawa ta goma.
Ƙungiyar mai suna 'The North-West Progressives Forum' ta gargadi zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu da kada ya kuskura ya ba da dama ga sauran yankunan kasar na shugabancin majalisar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban kungiyar, Nasir Danbatta da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a ranar Asabar 29 ga watan Afrilu, yace arewa maso yammacin kasar tafi kowane yanki ba da ƙuri'u wa jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa da ya gabata.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kungiyar dake arewa maso yamma tace babu wanda ya cancanci kujerar majalisar dattawa kamar tsohon gwamnan Zamfara.
Idan za a yi adalci, a ba Yari shugabancin majalisa
Ta kuma gargadi zababben shugana kasar Najeriya da ya tabbatar ya bai wa Abdulaziz Yari domin yankinsa ya ba da kaso mafi tsoka a cikin kuri'un da aka kada.
Kungiyar tace rashin adalci ne kawai zai sa a bai wa wani yanki na kasar nan shugabancin kujerar.
Ya ce:
"Muna bukatar a bamu shugaban majalisar dattawa a wannan yanki namu, kuma wanda muke so ya jagoranceta shine tsohon gwamnan jihar Zamfara"
Mai Neman Shugabancin Majalisar Dattawa Ya Kebe Da Shugaba Buhari, Ya Bayyana Yankin Da Ya Cancanci Kujerar
"Sakamako ya tabbatar da cewa arewa maso yamma ne yankin da yafi kowane bai wa Tinubu kuri'u wanda hakan ya sa suka fi cancanta a ba su wannan kujera.
"Duk da bama tsammanin Tinubu zai bai wa wani yanki wannan kujera, muna tunanin bai wa yankin arewa maso yamma shine adalci ga mutane da suka sha wahala."
'Yan Majalisa 18 Sun Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Abiya
A wani labarin, mambobin majalisar dokokin jihar Abia sun kaɗa kuri'ar tsige kakakin majalisar, Honorabul Chinedum Orji.
Mambobi 18 daga cikin 27 na majalisar dokokin ne suka amince da tsige shugaban majalisar yayin wani zaman gaggawa da suka yi a wani wuri da basu bayyana ba.
Asali: Legit.ng