Peter Obi Ya Sanya Labule Da Tinubu? Dan Takarar Na Labour Party Ya Bayyana Gaskiyar Abinda Ya Faru

Peter Obi Ya Sanya Labule Da Tinubu? Dan Takarar Na Labour Party Ya Bayyana Gaskiyar Abinda Ya Faru

  • Peter Obi, ɗan takarar jam'iyyar Labour Party a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, ya musanta sanya labule da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu
  • Obi, a cikin wata tattaunawa, ya kuma musanta cewa an cafke shi a UK. Inda ya ce jami'an shiga da fice na birnin Landan, sun tsayar da shi ne kawai domin bincike na yau da kullum
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa shi ba ɗan ƙasa bane a UK sannan ya mayar da iznin sa na zama a ƙasar lokacin da ya so barin ta
  • Abuja - Ɗan takarar jam'iyyar Labour Party a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, Peter Obi, ya musanta rahoton cewa ya gana da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A cewar rahoton Vanguard, Obi ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Channels tv, inda ya fayyace haƙiƙanin abinda ya faru tsakanin sa da jami'an shige da fice na UK, inda aka tsare shi kwanan nan.

Kara karanta wannan

To Fa: Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Ƙara Shiga Sabon Tasku Kan Ayyana Aishatu Binani

Peter Obi ya musanta ganawa da Bola Tinubu
Peter Obi ya musanta cewa ya sanya labule da Tinubu Hoto: Peter Obi
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na jihar Anambra, ya ce jita-jitar da ke yawo wacce aka sanya hoton sa da na Tinubu, wani ƙoƙari ne na ƴan adawa domin kawo ruɗani.

"Babu wanda na kai wa ziyara." A cewar tsohon gwamnan.

Jagoran na jam'iyyar Labour Party ya bayyana cewa a shirye ya ke ya mutunta doka sannan da tabbatar da cewa ƙarar da ya kai kotun ɗaukaka ƙarar zaɓen shugaban ƙasa an kammala ta yadda ya dace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ya ke magana kan ƙaƙanniƙayin da ya tsinci kansa a ciki a UK, Obi ya ce ba ya da izinin zama ɗan ƙasa a Burtaniya

A cewar sa ya mayar da izinin zama a ƙasar mara ƙarewa da ya ke da shi, ga hukumomin ƙasar lokacin da ya so barin ta bayan ya kwashe tsawon shekaru a ƙasar, cewar rahoton Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

"Zan Kwato Nasara Ta a Kotu" Dan Takarar Gwamnan APC a Jihar Arewa Ya Sha Alwashi

Peter Obi ya kuma musanta cewa an cafke shi a UK, inda ya bayyana cewa kawai an tsayar da shi ne domin yin binciken da aka saba a ofishin jami'an shige da fice na ƙasar a birnin Landan.

Akpabio Ya Sanya Labule Da Shugaba Buhari

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa tsohon minista kuma ɗaya daga cikin masu neman shugabancin kujerar majalisar dattawa, ya gana da shugaba Buhari.

Sanata Godswill Akpabio, ya ziyarci shugaba Buhari ne, domin shaida masa aniyar sa ta son zama sabon shugaban majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng