Yan Sandan Kasa Da Kasa Sun Gayyaci Kwamishinan Zaben Adamawa
- Yan sandan ƙasa da ƙasa (Interpol) sun gayyaci tsohon kwamishinan zaben jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari
- A wata takarda da mataimakin sufetan yan sanda ya rattabawa hannu, Ari zai amsa tambayoyi game da abinda ya aikata lokacin zaɓe
- Mista Ari, ya ja hankalin duniya bayan ya ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamna a Adamawa
Hukumar 'yan sandan ƙasa da ƙasa (Interpol) ta gayyaci dakataccen kwamishinan zaɓen INEC (REC) na jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari.
Interpol ta gayyaci kwamishinan zaɓen ne kan tuhumar da ke kansa game da abinda ya aikata a lokacin ƙarisa zaɓen gwamnan Adamawa ranar 14 ga watan Afrilu, 2023.
Tribune online ta rahoton cewa hakan na kunshe a wata wasiƙa daga Interpol mai ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Afrilu, 2023.
Wasiƙar ta buƙaci Mista Yunusa Ari ya bayyana domin amsa wasu tambayoyi a cibiyar hukumar tattara bayanai ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace rana Interpol ta umarci Ari ya bayyana gabanta?
Sai dai takardar ba ta bayyana ainihin ranar da kwamishinan zaɓen zai bayyana gaban Interpol ɗin ba.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Mataimakin sufetan yan sanda na ƙasa mai kula da harkokin Interpol, Garba Umar, ya rattaɓa hannu a kan takardar.
Yunusa Ari, wanda INEC ta dakatar daga matsayin kwamishinan zaɓe, ya shiga kanun labarai bayan ya ayyana Sanata Aishatu Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben Adamawa.
Ya sanar da sakamakon zaɓen gwamnan tun gabanin kammala tattara sakamako, kuma hakan ya saɓawa tanadin kundin zaɓe 2022.
Wasu bayanai sun nuna cewa bayan ayyana Binani, Ari ya bar jihar Adamawa a wani jirgi kuma har yanzun babu wanda ya san takamaiman inda ya shiga.
Bayin Allah Da Dama Sun Jikkata, Dukiyoyi Sun Salwanta a Wani Mummunan Fada Da Ya Barke a Jihar Arewa
Amma wasu majiyoyi masu kusanci da dakataccen kwamishinan sun yi iƙirarin cewa ba guduwa ya yi ba, kamar yadda The Cable ta rahoto.
NDLEA Ta Faɗa Wa Kotu Gaskiya
A wani labarin kuma Hukumar NDLEA Ta Faɗa Wa Kotu Gaskiya Kan Karar da PDP Ta Shigar da Bola Tinubu
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta roki babbar Kotun tarayya ta kori ƙarar da PDP ta shigar da zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
PDP da sanata Dino Melaye sun kai ƙarar Tinubu gaban Kotu, inda suka nemi ta tilasta wa NDLEA ta kamo tsohon gwamnan kana ta gurfanar da shi.
Asali: Legit.ng