‘Dan Majalisar Kano da Ake Zargi da Kisan Kai Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa

‘Dan Majalisar Kano da Ake Zargi da Kisan Kai Ya Fito Takarar Shugaban Majalisa

  • Alhassan Ado Doguwa ya bada sanarwar cewa zai yi takarar shugabancin majalisar wakilan tarayya
  • Yanzu haka ana binciken ‘Dan majalisar na Tudun Wada/Doguwa da zargin kashe mutane lokacin zaben 2023
  • Hon. Doguwa ya karyata zargin, ya kuma kalubalanci wadanda suka yi masa ‘kazafi’ da su kawo hujja

Abuja - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya shiga cikin masu neman shugabancin majalisa ta goma.

Daily Trust ta rahoto shiga takarar Honarabul Alhassan Ado Doguwa mai wakiltar mazabar Tudun Wada/Doguwa na jihar Kano a jam’iyyar APC.

‘Dan majalisar ya aika takarda yana mai sanar da hakan ga ‘yan majalisar tarayya masu ci da zababbun ‘yan majalisa domin su mara masa baya.

Alhassan Ado Doguwa yake cewa ya fito neman wannan mukami ne saboda kishin gyara kasarsa.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Ja Hankalin Atiku da Obi, Ya Faɗi Abinda Ya Rage Musu Kan Zaben 2023

Bayan mutanen mazabunsu sun kada masu kuri’a a zaben da ya gabata, ‘Dan siyasar ya taya abokan aikinsa murna, ya ce shugabanci nauyi ne.

‘Dan Majalisar Kano
Alhassan Ado Doguwa a mazabarsa Hoto: www.voahausa.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasikar Alhassan Ado Doguwa

Ina mai taya ku murnar lashe zabe da ku ka yi na zuwa majalisar tarayya ta goma.
An fara gwagwarmayar gyaran kasa, saboda haka a wannan karo mun zo domin wakiltar mutannen Najeriya da suka yarda da mu.
Ina so yi amfani da wannan dama wajen sanar da ku burina na neman takarar shugaban majalisar wakilan tarayya na Najeriya.
Sha’awar da na ke da shi na gyara kasa, shi ya tunzuro ni wajen shiga takarar kujerar nan.

- Alhassan Ado Doguwa

A ajiye duk wani bambanci

A daidai wannan gaba da ake da mabanbantan ra’ayi, Arewa Radio ta rahoto Doguwa yana cewa ya kamata a hada-kai domin a taimaki talakan Najeriya.

Kara karanta wannan

Zargin Kisan Kai: Doguwa Ya Shiga Matsala Yayin Da Kotu Ta Ba Atoni Janar Na Jihar Kano Sabon Umurni

Hon. Doguwa ya yi kira ga ‘yan majalisa su yi watsi da bambancin addini, kabilanci, bangaranci da na siyasa wadanda duk za su iya hana cigaban kasa.

"Nagode, ina sake taya ku murna, ina sa ran ganin ku a majalisar tarayya."

- Alhassan Ado Doguwa

Zargin kisan kai

A watan Fubrairu ne 'Yan sanda su ka kama shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, a kan zarginsa da hannu a kisan kai a garin Tudun Wada.

Rahoton ya ce ana kuma tuhumar Alhassan Ado Doguwa da kona sakatariyar jam'iyyar NNPP, zargin da ya karyata, ya ce ko fara bai hallaka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng