Tinubu: An Bukaci Hukumomin Tsaro Su Kara Ba Zababben Shugaban Kasa Kariya
- Kungiyar MURIC ta ja hankalin DSS da sauran hukumomin tsaro da su su kara tsaurara matakan tsaro ga Bola Tinubu da Kashim Shettima
- Ishaq Akintola, daraktan kungiyar yace jan hankalin ya zama dole saboda barazanar tsaro da kalaman cin amanar kasa da ke fitowa daga bangaren yan adawa
- Farfesan ya ce budaddiyar barazanar ta yi kaifi da yawa cewa ba abu ne da za a iya watsi da ita ba
An ja hankalin rundunar tsaron farin kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro da su tsaurara matakan tsaro a kan Bola Tinubu, zababben shugaban kasa da zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ce ta yi jan hankalin a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu, PM News ta rahoto.
Kungiyar ta jaddada cewar kiran ya zama dole saboda barazanar tsaro da kalaman cin amana da ke fitowa daga bangaren abokan hamayya, rahoton The Guardian.
Dalilin da yasa MURIC ta koka kan tsaron Bola Tinubu da Kashim Shettima
Farfesa Ishaq Akintola, daraktan kungiyar ne ya yi kirana a cikin wata sanarwa da ya fitar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
MURIC ta bayyana tashin hankalin da ke fitowa daga bangaren adawa a matsayin wanda ya yi kamari kuma cewa za a iya yanke shi da wuka.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"Muna ganin ya zama dole a ankarar da kasar, musamman hukumomin tsaro, game da munanan alamu da ke fitowa daga bangaren siyasar Najeriya. Barazana da dama sun billo kan gabatowar ranar rantsar da wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023."
Sanarwar ya kuma bayyana barazanar da ke kewaye da zababben shugaban kasar da mataimakinsa a matsayin irinsa na farko bayan kaddamar da wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Tun bayan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, jam'iyyun adawa sun yi watsi da nasararsa.
Ba mai hana rantsar da Tinubu sai wani ikon Allah, Keyamo
A wani labarin, karamin ministan kwadago, Festus Keyamo ya bayyana cewa babu abun da zai hana a rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu sai dai wani ikon Allah.
Asali: Legit.ng