Mataimaki Ya Kai Shugaban Jam’iyyar APC Kotu Yayin da Rikicin Cikin Gida Ya Yi Kamari

Mataimaki Ya Kai Shugaban Jam’iyyar APC Kotu Yayin da Rikicin Cikin Gida Ya Yi Kamari

  • Sabanin Salihu Mohammed Lukman da Abdullahi Adamu a Jam’iyyar APC NWC ya yi muni
  • Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa ya yi karar Adamu da Iyiola Omisore
  • Lukman ya sanar da Jagororin APC cewa Shugaba da Sakataren jam’iyya na kasa sun bijirewa doka

Abuja - Rikicin da ake fama da shi a jam’iyyar APC ya karu ne a maimakon ya lafa, lamarin ya kai Alhaji Salihu Mohammed Lukman ya tafi kotu.

A rahoton Daily Trust, an ji Mataimakin shugaban APC mai wakiltar Arewa, Salihu Mohammed Lukman ya shigar da karar shugaban jam’iyya na kasa.

Salihu Lukman ya dumfari kotun tarayya mai zama a garin Abuja, zai yi shari’a da jam’iyyar APC, Shugabanta, Sakatare na kasa da hukumar INEC.

A wannan kara mai lamba FHC/ABJICS/ 573 da aka shigar ta hannun Lauya Mohammed Kabir Abdullahi an zargi APC da kin kiran taron NEC.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Shugaban APC Ya Yi Magana Kan Wanda Za'a Baiwa Shugabancin Majalisa Ta 10

Bukatar Lauya mai kara

Mataimakin shugaban na jam’iyya mai mulki yana so kotun tarayyar ta tursasawa jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore shirya taron koli.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar ta ce Lukman yana ganin akwai bukatar ayi wannan zama domin a ji inda jam’iyya ta kwana domin tun Afrilun 2022 rabon da majalisar ta zauna.

Shugaban Jam’iyyar APC
'Yan APC a kamfe Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Baya ga haka, tsohon shugaban na kungiyar PGF ya bukaci kotu ta umarci shugabannin jam’iyyar APC su fadi yadda ake bi wajen zabo shugabanni.

Har ila yau, Vanguard ta ce ‘dan majalisar na NWC yana so Alkali ya raba masu gardama a kan abin da sashe na 25.2 na dokar jam’iyyar APC yake nufi.

Mohammed Kabir Abdullahi. Esq ya ce tsarin jam’iyya ya bukaci a rika yin bayanin kudin da aka kashe lokaci zuwa lokaci, abin da ya ce ba ayi ba a yanzu.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar ‘Hujjar’ da ke Nuna Magudin Bola Tinubu

Buhari ya samu labari

Premium Times ta ce a wata wasika da ya aikawa Muhammadu Buhari, Asiwaju Bola Tinubu da Gwamnonin APC, Lukman ya sanar da su cewa ya je kotu.

Wasikar ta hada da shugabannin APC inda aka ji ‘dan siyasar yana zargin jagororin NWC da daukar doka hannunsu, su na yin duk abin da suka ga dama.

APC ta tafi kotu a Zamfara

An ji labari Gwamnan Zamfara ya nuna su na sa ran jam’iyyar APC ta koma kan karagar mulki, an je kotun karar zabe domin kalubalantar nasarar PDP.

Wani Mai ba Gwamnan jihar Zamfara shawara ya ce babu ta yadda mutanen kirkin jihar Zamfara za su ki zaben Gwamna Bello Matawalle ganin irin aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng