Ku Kara Hakuri Da APC Kan Raba Mukaman Majalisa Ta 10, Abdullahi Adamu
- Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya roki 'yan Najeriya su kara hakuri da jam'iyya mai mulki kan batun shugabancin majalisa
- Adamu ya ce har yanzun jam'iyyar ba ta gama shagalin murnar nasarorin da ta samu a babban zaben 2023 ba
- Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya dawo gida Najeriya
Abuja - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya roki 'yan Najeriya su ƙara hakuri da jam'iyyar game da batun raba shugabancin majalisa ta 10.
Channels tv ta ce Adamu ya bayyana haka ne ranar Laraba jim kaɗan bayan ganawa da zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Kashin Shettima.
Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan zama wanda ya gudana cikin sirri ya samu halartar shugabannin APC da masu ruwa da tsaki ciki har da shugabannin majalisa ta 9.
Duk da ba'a bayyana abinda aka tattauna a taron ba, wanda ya shafe kusan awa guda, wasu majiyoyin sun ce zaman na da alaƙa da raba muƙaman majalisar tarayya ta 10.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga taron, Sanata Adamu, ya ce har yanzun jam'iyyar APC na cikin murnar nasarar da ta samu a babban zaɓe.
Shugaban APC ya ce:
"Ya kamata yan Najeriya su ƙara hakuri da jam'iyya, mu ƙara jira, abinda zai wa ƙasar nan kyau shi ne muradin mu a jam'iyya. A yanzu dai muna shagalin murna ta nasarar da APC ta samu."
Jiga-jigan da suka halarci taron
Daga cikin kusoshin APC da suka hallara wurin taron sun ƙunshi, gwamna AbdulRazak Abdulrahman na jihar Kwara, mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) da shugaban APC, Abdullahi Adamu.
Sauran sun haɗa da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, mataimakinsa, Sanata Ovie Omo-Agege, kakakin majalisar wakilai, Femi Gabajabiamila da kakakin majalisar dokokin Kaduna, Yusuf Zailani.
Da yuwuwar Tinubu ya yaƙi Buhari - Bwala
A wani labarin kuma Tsagin Atiku Abubakar Ya Tsoma Baki a Mulkin Tinubu, Ya Fallasa Shirin Yaƙar Buhari Bayan Ya Sauka
Na kusa da ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi hasashen zaman doya da manja tsakanin Buhari da Tinubu bayan 29 ga watan Mayu.
Daniel Bwala ya ce a ko da yaushe shugaba Muhammadu Buhari na cewa PDP ce ta jefa Najeriya cikin ƙaƙanikayi, idan Tinubu ya hau mulki wa zai ɗora wa laifin.
Asali: Legit.ng