Zababbun ‘Yan NNPP, LP, da PDP Za Su Goyi Bayan ‘Dan APC a Zaben Majalisar Tarayya

Zababbun ‘Yan NNPP, LP, da PDP Za Su Goyi Bayan ‘Dan APC a Zaben Majalisar Tarayya

  • Wasu zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya sun fadawa Duniya wanene ‘dan takaransu a 2023
  • ‘Yan siyasar nan da aka zaba a jam’iyyun NNPP, LP, da PDP za su goyi bayan Muktar Aliyu Betara
  • Ismail Haruna Dabo ya ce Hon. Muktar Aliyu Betara ne zabinsu, kuma za su fara yawon tallata shi

Abuja - Wasu daga cikin zababbun ‘yan majalisar wakilan tarayya, sun nuna inda suka sa gaba yayin da aski ya zo gaban goshi a neman shugabanci.

A rahoton da Daily Trust ta fitar, an fahimci wadannan zababbun ‘yan majalisa sun nuna cewa goyon bayansu yana ga Hon. Muktar Aliyu Betara ne.

‘Yan siyasar za su marawa Muktar Aliyu Betara baya, sannan su fara yawo a duk lungu da kwararon mazabun Najeriya domin ganin sun tallata shi.

A cewarsu, ba su kaunar mugu mai muzgunawa mutane ya zama shugaban majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An Kori Mataimakin Shugaban APC Da Wasu 7

Farin jinin Muktar Aliyu Betara

Honarabul Betara mai wakiltar mazabar Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar daga jihar Borno shi ne shugaban kwamitin da ke kula da harkar kasafin kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan majalisar yana da farin jini, ana yi maso kallon ‘yan gaba-gaba a takarar shekarar nan.

Majalisa
Shugaban Majalisar Wakilai Hoto: @femigbaja
Asali: Twitter

Sababbin ‘yan majalisar da za a rantsar a Yunin 2023 da suke tare da Betara sun fito ne daga APC mai rinjaye da jam’iyyun adawa na: NNPP, PDP da LP.

Shugaban wannan tafiya, Ismail Haruna Dabo ya shaidawa manema labaran cewa za su ajiye duk wani sabani na jam’iyya, su marawa Hon. Betara baya.

A zagayen da za su fara a bangarori shida na kasar nan, Ismail Haruna Dabo ya ce za su yi kokari wajen wayar da kan al’umma a kan takarar ‘dan majalisar.

Wadanda suke tare da Ismail Dabo su na ganin shugaban kwamitin kasafin kudin yana da abin da ake bukata wajen jagorantar mutane 360 da ke majalisa.

Kara karanta wannan

Allah-wadai: Manyan APC a kananan hukumomi 2 sun tamke sanata, sun kore daga cikinta

Kamar yadda ku ka sani, ba mu son mugu a matsayin shugaban majalisar tarayya ta goma.
Shiyasa (Betara) ya zama ‘dan takararmu, kuma za mu fara kamfe daga Enugu.

- Ismail Haruna Dabo

Jaji, Wase da Betara ne a gaba

Labari ya zo irin haka a baya, an samu rahoto wasu wadanda aka yi a majalisa da su a 2007 zuwa 2019, su na goyon bayan Hon. Muktar Betara Aliyu.

Ahmed Wase zai gwabza Aliyu Betara, da Aminu Sani Jaji kafin ya iya zama Shugaban Majalisa, ana ganin wadannan ukun sun fi karfi a takarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng