Zaben Majalisa: An Bar Apc da Ciwon Kai, Mutanen Arewa Maso Yamma Sun Huro Wuta

Zaben Majalisa: An Bar Apc da Ciwon Kai, Mutanen Arewa Maso Yamma Sun Huro Wuta

  • ‘Yan yankin Arewa maso yamma ba su da niyyar hakura da kujerar shugaban majalisar dattawa
  • Idan kujerar ta fada hannun yankin, zai kasance Musulmi yake rike da kujeru uku mafi daraja
  • Tikitin Musulmi da Musulmi da jam’iyyar APC tayi ya jawo ana so Kirista ya rike Majalisar dattawa

Abuja - Akwai sabuwar tirka-tirka a cikin jam’iyyar APC mai mulki a dalilin zaben shugaban majalisar dattawa da ake shirin yi a Najeriya.

Sanatocin da suke harin kujerar Ahmad Lawan sun dage domin ganin sun samun nasara, Daily Trust ta ce APC ba ta ce komai a kan batun ba.

Jam’iyya mai-ci da kuma Bola Ahmed Tinubu wanda shi ne shugaban kasa mai jiran gado ba su tsaida magana a kan yadda za a raba kujeru ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi Zai Janye Karar Da Ya Shigar Kan Tinubu? Labour Party Ta Koka

Babu wanda ya san matsayar zababben shugaban kasar da jam’iyyarsa ta APC kan siyasar majalisa, hakaya jawo ‘yan takara suka yawaita.

Bangaranci ko cancanta?

Yayin da wasu ke neman ayi la’akari da yanki a wajen zakolo shugabannin majalisar tarayyar, wasu sun bada shawarar a bar cancanta tayi aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saukinta Bola Tinubu ya dawo, wata majiya ta shaidawa jaridar cewa APC za ta zauna a kan maganar domin a ware kujerun zuwa bangarori.

Zaben Majalisa
Bola Tinubu da Shugaban Majalisar Dattawa Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Wasu masu ruwa da tsaki da Sanatocin da suka fito daga Arewa maso yamma, sun ce a yankinsu ya kamata a samu sabon shugaban majalisar dattawa.

Masu ra'ayin nan su na ganin a tarihi, ba a taba samun shugaban majalisar dattawa daga Kano, Katsina, Kaduna, Jigawa, Sokoto, Kebbi ko Zamfara ba.

Arewa maso yamma ta bada gudumuwa a 2023

Kara karanta wannan

Waiwaye Ga Mulkin Buhari: Manyan Alkawura 3 Da Buhari Ya Dauka, Amma Ya Gaza Cika Wa

Sannan a yankinsu jam’iyyar APC ta samu kuri’u 2,653,235 a zaben shugaban kasa, adadin ya zarce abin da Tinubu ya samu daga Kudu maso yamma.

Ana kalubalantar masu akasin wannan tunani da cewa kuri’u 799, 957 jam’iyya mai rinjaye daga jihohin Kudu maso kudu da ake so a warewa kujerar.

Kusan wanda ya yi fice a cikin masu neman kujerar nan daga yankin shi ne Barau Jibrin (Kano ta Arewa), Sanatan ya shafe shekaru 12 a majalisa.

Tasgaron ita ce Sanata Barau Jibrin Musulmi ne kamar Bola Tinubu da Kashim Shettima, babu mamaki Kiristoci su koka cewa an yi watsi da su.

'Yan Majalisa v Gwamnonin APC

Ana da labari akwai gumurzu a Majalisar tarayya, domin an ki daukar shawarwarin da Kungiyar Gwamnonin APC ta ba zababben shugaban Najeriya.

Watakila 2023 ta zama kamar 2019, Ibo daga yankin Kudu ya zama Shugaban majalisar dattawa, Bayarabe da 'Dan Arewa kuma us na Aso Rock.

Kara karanta wannan

Bayan Kwanaki 33 a Kasar Waje, An Sanar da Lokacin da Bola Tinubu Zai Dawo Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng