Shawarar da Gwamnoni Suka Ba Tinubu Tana Neman Jawo Yaki a Majalisar Tarayya

Shawarar da Gwamnoni Suka Ba Tinubu Tana Neman Jawo Yaki a Majalisar Tarayya

  • Zababbun ‘Yan majalisa da wadanda ke barin kan mulki sun tofa albarkaci a kan zaben wannan karo
  • ‘Yan majalisar ba su goyon bayan Gwamnonin APC da suka ba Bola Tinubu shawarar yadda za ayi rabo
  • Kason kujerun zai zo da sarkakiya saboda Musulmai za su dare kujerar shugaban kasa da mataimaki

Abuja - Wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilan tarayya sun soki yadda Gwamnonin jihohi suka bada shawarar ayi kason mukaman da ake da su.

Rahoton Premium Times ya nuna shawarar Gwamnonin APC a karkashin kungiyar PGF ba ta samu shiga ba, ‘Yan PDP da APC sun soki matsayar.

Alal misali, Honarabul Akin Alabi (APC, Oyo) ya yi watsi da wadannan shawarwari da aka ba Bola Tinubu a matsayinsa na zababben shugaban kasa.

Alabi ya nuna zai yi wahala jam’iyyar APC ta ware manyan kujerun majalisa ga yankin Arewa, la’akari da tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi.

Kara karanta wannan

Barka da Sallah: Atiku Ya Fadi Abin da Yake Damunsa, Tinubu Ya Yi kira ga Musulmi

Addini zai yi tasiri

‘Dan majalisar na Egbeda/Ona-Ara ya yi bayani ne a taron da jaridar ta shirya a Twitter.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake magana ranar Asabar, Alabi ya ce ganin Tinubu da Kashim Shettima Musulmai ne, kyau shugaban majalisar dattawa ya zama Kirista.

Majalisar Tarayya
Shugaban majalisa a zama Hoto: @SpeakerGbaja
Asali: UGC

A ba Ibo kujerar ne mafita

Shi kuwa Rolland Igbakpa (PDP, Delta) ya bada shawara ayi la’akari da Sanatocin Kudu maso gabas saboda korafin da mutanen yankin Ibo suke yi.

‘Yan Kudu maso gabashin Najeriya su na kukan an maida su saniyar ware, har su na neman a raba kasa, watakila ba su kujerar ya rage rashin jituwar.

Duk da ba daga yankin ya fito ba, Honarabul Igbakpa yana ganin hakan zai kawo zaman lafiya. Hon. Ali JC Isa ya dauki wata matsaya dabam a kai.

A binciken da Vanguard tayi, ta fahimci ‘yan majalisa masu barin gado da zababbu da-dama ba su tare da Gwamnoni a kan shawarar da suka ba Tinubu.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Nada Kyari, Marwa, ‘Yaradua da Mutum 11 a Kwamitin Karbar Mulki

Hon. Ben Igbakpa yana so a maimaita irin na 1999, shugaban majalisar dattawa ya zama Ibo, sai a dauko shugaban majalisar wakilai daga jihohin Arewa.

Sai yadda jam'iyya ta fada - Kalu

Hon. Benjamin Kalu mai neman shugaban majalisar wakilai yana da ra’ayin wuka da nama yana hannun jam’iyya, musamman wanda take da rinjaye.

An rahoto Hon. Kingsley Chinda yana cewa za su goyi baya a raba kujerun tsakanin bangarorin kasar nan, muddin haka zai kawo kwanciyar hankali.

Hon. Victor Afam Ogene wanda aka zaba ya wakilci mazabar Ogbaru ya ce babu dalilin da Gwamnonin APC za su fadawa majalisa abin da za tayi.

Arewa maso yamma sun bada kuri'u

An ji labari Sahabi Sufyan, daya daga cikin matasan APC ya shaidawa Legit.ng Hausa Aliyu Wammako ya cancanci rike majalisar dattawan Najeriya.

Baya ga cewa da shi aka kafa APC, Sufyan ya ce Sanatan ya bada gudumuwa, kuma cikakken ‘dan siyasa ne daga yankin da suka taimaka a zabe.

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Majalisa Ya Jefa Wasu Ministoci a Matsala, An Fito da Zargin $200m

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng