Matashin Da Ya Ci Zaben Dan Majalisar Tarayya a Taraba Ya Rasu
- Ana cikin shagalin ƙaramar Sallah, Allah ya yi wa zababben ɗan majalisar wakilan tarayya a jihar Taraba rasuwa
- Ɗan siyasan, wanda ake kallon yana ɗaya daga cikin matasan da zasu shiga majalisa ta 10, ya rasu a wani Asibiti a Abuja
- Isma'ila Maihanci, ya rasu yana da shekara 36 a duniya kuma ya rike muƙaman siyasa a zamanin rayuwarsa
Taraba - Zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya, Isma'ila Maihamci, ya riga mu gidan gaskiya.
Daily Trust ta rahoto cewa Mamacin ya rasu yana da shekaru 36 a duniya. Kafin ya koma ga Allah, Maihanci ya ci zaɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Jalingo/Yorro/Zing a Taraba.
Isma'ila Maihanci, wanda ya samu nasarar zama ɗan majalisar tarayya a inuwar jam'iyyar PDP, ya rasu ne da sanyin safiyar yau Asabar, 22 ga watan Afrilu, 2023.
Rahotanni sun nuna cewa za'a yi masa jana'iza kamar yadda shari'ar Addinin Musulunci ta tanada nan da Anjima a yau Asabar a gidansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ta rahoto cewa ɗan siyasan ya koma ga mahalincinsa ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani Asibiti da ba'a faɗi sunansa ba a birnin tarayya Abuja.
Wani hadimin marigayi zababɓen ɗan majalisar, wanda ya tabbatar da rasuwar, ya ce za'a masa jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya koyar a binne sa a maƙabartar tarayya da ke Abuja
Wanda aka haifa ranar 22 ga watan Oktoba, 1986, Ɗan siyasan kuma ɗan kasuwa ya yi aiki a matsayin mai baiwa gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, shawara ta musamman.
Haka zalika, marigayi Maihanci ya rike kujerar Sakataren jam'iyyar PDP reshen jihar Taraba a zamanin rayuwarsa.
Ganduje Ya Bukaci Abba Gida-Gida Ya Ƙarasa Wasu Ayyuka
A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje Ya Bukaci Abba Gida-Gida Ya Ƙarasa Wasu Ayyuka a Kano
Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya taya ɗaukacin al'ummar Musulmai musamman mazauna Kano barka da ƙaramar Sallah, Allah ya maimaita mana.
A sakon Ganduje ranar Jumu'a, ya yi kira ga sabon gwamna idan ya kafa gwamnati ya ƙarisa muhimman ayyukan da gwamnati mai ci ta fara.
Asali: Legit.ng