Eid el-Fitr: Shugaba Buhari da Bola Tinubu Sun Yi Magana Ta Waya, Shehu

Eid el-Fitr: Shugaba Buhari da Bola Tinubu Sun Yi Magana Ta Waya, Shehu

  • Shugaba Muhammadu Buhari da Bola Tinubu sun zanta ta wayar salula bayan gama Azumin watan Ramadan
  • Garba Shehu ya ce shugabannin biyu sun gode wa Allah da kuma taya juna murnar zuwa Sallah ƙarama
  • Buhari ya bayyana cewa a shirye yake ya miƙa wa Bola Ahmed Tinubu mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tattauna ta wayar salula da zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ranar ƙaramar Sallah 21 ga watan Afrilu, 2023.

Buhari da shugaban ƙasa mai jiran gado sun yi waya ne domin taya juna murnar zuwan Eid-El-Fitr watau ƙaramar Sallah bayan gama Azumin watan Ramadan.

Tinubu da Buhari.
Shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu, da shugaba Muhammadu Buhari Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

Kakakin shugaban ƙasa, Mallam Garba Shehu, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook ranar Jummu'a 21 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Dau Zafi, Ya Yi Wa Shugaba Buhari Kakkausan Martani

Shehu ya ce, "Dukkan shugabannin biyu sun kara gode wa Allah wanda da izininsa ne suke raye har suka sake shaida wannan rana kuma sun yi wa ƙasa Addu'a."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika kakakin shugaban kasan ya ƙara da cewa yayin hirar manyan mutanen biyu, Buhari ya kara jaddada shirinsa na tarban Tinubu zuwa fadar shugaban ƙasa ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Sanarwan da Shehu ya rabbaɓa hannu kuma Femi Adesina, hadimin Buhari ya wallafa a shafinsa ta ce:

"Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban ƙasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Tinubu, sun gaisa sun yi wa juna barka da Sallah ta wayar tarho bayan kammala azumin Ramadan ranar Jummu'a da safe."
"Shugabannin sun ƙara gode wa Allah da ya barsu a raye har suka shaida wannan rana kuma sun yi wa ƙasa Addu'ar samun daidaito da kuma ci gaba."
"Shugaba Buhari ya ƙara nuna kudirinsa na shirin tarban Bola Tinubu zuwa fadar shugaban ƙasa a matsayin shugaban Najeriya ranar 29 ga watan Mayu, 2023."

Kara karanta wannan

Ranar Rantsuwa: Tinubu Ya Kafa Wani Muhimmin Kwamiti Domin Amsar Mulki a Hannun Buhari

A wani labarin kuma Ministan Buhari Ya Cire Tsoro, Ya Faɗi Babban Abinda Ya Yi Nadama A Mulkinsa

Ministan Abuja, Muhammed Bello, ya jagoranci tawagarsa zuwa fadar shugaban ƙasa domin yi wa Buhari barka da sallah.

Ya bayyana cewa ya yi baƙin cikin gaza shawo kan Sanatan Abuja ya bar jam'iyyar PDP zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262