Bola Tinubu Ya Nada Kyari, Marwa, ‘Yaradua da Mutum 11 a Kwamitin Karbar Mulki

Bola Tinubu Ya Nada Kyari, Marwa, ‘Yaradua da Mutum 11 a Kwamitin Karbar Mulki

  • Asiwaju Bola Tinubu ya fitar da sunayen wasu da za su taya shi aiki wajen karbar ragamar mulki
  • A kwamitin akwai ‘danuwan tsohon Shugaban kasa, zababben Sanatan Katsina, Abdulaziz Yar’adua
  • Sanata Abubakar Kyari, Stella Okotete da Bayo Onanuga sun samu matsayi mai tsoka a kwamitin

Abuja - Asiwaju Bola Tinubu wanda zai dare kan karagar mulki, ya sanar da mutanen da za su shiga cikin kwamitin da zai yi masa aikin karbar shugabanci.

A yammacin Alhamis, rahoto ya zo daga Vanguard cewa kwamitin mai kunshe da mutum 13 zai yi wa Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima sharan fage.

A wasikar da ya aikawa Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Bola Tinubu ya sanar da Abubakar Kyari a matsayin shugaban harkar kudi a kwamitin.

Tsohon Sanatan Borno ta Arewa kuma mataimakin shugaban APC na yankin Arewa, Abubakar Kyari ne zai jagoranci sha’anin kasafin kudi da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Ka zo Ukraine: Shugaba Zelensky ya taya Tinubu murnar lashe zabe, ya yi masa gayyata ta musamman

Akwai Shugaban APC, Darektar NEXIM

Darektar cigaban kasuwanci ta bankin NEXIM, Stella Okotete za ta zama Shugabar kwamitin tsare-tsare, sa ido da kuma rubuce-rubuce a wannan kwamiti.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Makinde Araoye wanda ya taba yin takarar Gwamna a Ekiti a APC, zai kula da abubuwan da suka shafi wurin zama a bikin rantsar da sabon shugaban kasa.

Tinubu
Bola Tinubu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Nairaland ta ce Bayo Onanuga zai zama Shugaban kwamitin yada labarai da hulda da jama’a.

Sauran wadanda ke cikin kwamitin

Kwamishinar lafiya ta Kuros Riba kuma shugaban mata ta jam’iyyar APC, Dr Betta Edu za ta kula da kwamitin lafiya, Zainab Buba Marwa za ta kula da liyafa.

Kanal Abdulazeez Yar’Adua mai ritaya aka ba nauyin abin da ya shafi tsaro da fareti da za ayi.

Samira Saddik aka bari da harkar yara, Abuh Andrew Abuh kuma masaukin baki, Dr. Danladi Bako zai shirya lacca, gayyata tana karkashin Donald Wokoma.

Kara karanta wannan

Zaben Adamawa: Zababben Shugaban kasa, Tinubu ya yi kira ga ‘Yan Sanda da Binani

Hadiza Mohammed Kabir za ta kula da Sufuri da zirga-zirga, sannan Bishof Adegbite da kuma Imam Faud su jagoranci sha’anin coci da sallar juma’a a kwamitin.

Matsayar da aka dauka a FEC

An ji labari gwamnatin tarayya za ta gina titunan 737.242km a Kano, Kaduna, Borno da wasu Jihohi 11. Babatunde Fashola ya ce za a kashe N1, 535, 154, 247, 234.48.

Shugaban kasa yana Saudiya a lokacin, saboda haka Yemi Osinbajo ya dauki matakin yayin da Bola Tinubu yake shirin karbar mulki a ranar 29 ga watan Mayu 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng