Saura Kwana 40 a rantsar da Tinubu, Buhari Ya Amince A Gina Titunan Naira Tiriliyan 1.5

Saura Kwana 40 a rantsar da Tinubu, Buhari Ya Amince A Gina Titunan Naira Tiriliyan 1.5

  • A zaman FEC da Ministocin tarayya suka yi jiya, an yarda NNPCL ya kashe N1.5tr wajen yin tituna
  • Ministan ayyuka da gidajen Najeriya, Raji Babatunde Fashola SAN ya tabbatar da haka bayan taron
  • Edo da Delta su na cikin jihohin da za su amfana da wadannan manyan hanyoyi da za a gina a kasar

Abuja - Majalisar zartarwa ta kasa watau FEC, ta amince a batar da Naira Tiriliyan 1.535 wajen ginawa da gyara wasu tituna 11 a fadin Najeriya.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Alhamis cewa za ayi duka wadannan kwangiloli ne a karkashin tsarin harajin kamfanin mai na kasa watau NNPCL.

Ministan ayyuka da gidaje na kasa, Raji Babatunde Fashola SAN ya ce kudin za su tafi wajen gina manya-manyan tituna na tsawon kilomita fiye da 700.

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Majalisa Ya Jefa Wasu Ministoci a Matsala, An Fito da Zargin $200m

Majalisar FEC ta yi na’am da wadannan kwangiloli ne yayin da kwanaki 40 suka ragewa Muhammadu Buhari ya mikawa Bola Tinubu mulki.

Aiki ya kusa zuwa karshe

An rahoto Fashola yana cewa ba da dadewa ba za a kammala aikin da zai hada jihohi 11 da juna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan ya ce daga cikin jihohin da za su amfana da titunan akwai Kano, Kaduna, Borno Adamawa, haka zalika akwai jihohin Edo da kuma Delta.

FEC..
Ministoci a taron FEC Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Sun ta ce a watan Junairun 2023 ne FEC ta fara amincewa da wata takarda da NNPC ta kawo, ta na neman kashe Naira tiriliyan 1.9 wajen ayyukan tituna.

Wannan shi ne kashi na biyu na aikin da aka fito da shi da nufin gina abubuwan more rayuwa.

Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman da aka yi a makon nan domin Muhammadu Buhari ya na Saudi Arabiya.

Kara karanta wannan

Bayan Kwashe Shekaru Ana Aiki, Daga Karshe Ministan Buhari Ya Bayyana Ranar Kammala Titin Kaduna-Kano

Sauran matsayar da aka dauka

Baya ga tituna, majalisar Ministocin ta amince da bukatar wasu mutane 317 da suka nemi zama ‘Yan Najeriya, FEC ta ba su damar bayan ganin cancantarsu.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya ce wadanda aka ba shaidar zama ‘Yan Najeriya ta hanyar haihuwa ko rajista, sun cancanci zama ‘yan kasar.

A taron ne gwamnatin tarayya ta amince ayi amfani da na’urorin zamani domin maganin gobara.

Badakalar saida danyen mai

Rahoto ya zo cewa Babban Lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami da Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed sun shiga uku.

‘Yan majalisar tarayya su na zargin Ministocin da batar da $200m ba tare da an yi kasafi ba. Naira Biliyan 92 ake tunanin an sha kwana da su daga saida mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng