Shugabancin Kasa: Buhari Da Sauran Yan Takarar Shugaban Kasa Da Suka Zub Da Hawaye Kan Talaka a Talbijin
- Lamarin zabe a Najeriya kan dauki salo iri-iri a duk lokacin da guguwar zabe ta kado domin yan siyasa kan bi kowace hanya wajen shawo kan masu zabe don su zabe su
- Daya daga cikin abubuwan da ke kara ta'azarra siyasar kasar shine yadda yan siyasa ke nuna karayar zuciya, lamarin da ya fara da shugaba Buhari bayan zaben 2011
- Babban Janar din ya sharbi kuka a 2012 bayan ya sha kaye a kotun koli sannan ya yi alkawarin ba zai sake takara ba amma ya dawo ya zama shugaban Najeriya a 2015
Tun bayan dawowar damokradiyyar Najeriya a 1999, yan siyasa na ta amfani da dabaru daban-daban don shawo kan masu zabe kan dalilin da zai sa a zabe su.
Daya daga cikin wadannan dabarun shine nuna tausayin talaka a shirin kai tsaye na gidan talbijin, musamman ma kuka. Wannan ya zama tuwan dare a tsakanin yan takarar shugaban kasa, amma har yanzu yan Najeriya basu san da haka ba.
Ga jerin yan takarar shugaban kasa da suka taba sharbar kuka a talbijin na kasa:
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya mai barin gado shine dan takarar shugaban kasa na farko da ya fara sharbar kuka a talbijin na kasa bayan ya fadi zabe a karo na uku a 2012, yana mai tausayawa kasar da alkawarin cewa ba zai sake yin takara ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai a yayin shirye-shiryen zaben 2015, Buhari ya yi maja mai karfi da jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) inda ya zama shugaban kasar Najeriya a wani nasara mai cike da tarihi.
Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu shine mutum na biyu da ya sharbi kuka a talbijin na kasa.
Bayan ya yanki tikitin kara a PDP a 2018, tsohon mataimakin shugaban kasar ya sharbi kuka a shirin kai tsaye na gidan talbijin amma kuma sai ya fadi zabe a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu shima ya sharbi kuka a talbijin a jawabinsa na farko a Abuja.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi taron manema labarai kwanaki 3 bayan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da wanda ya lashe zaben.
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu daga cikin yan takarar shugaban kasa a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu sun garzaya kotu inda suke kalubalantar ayyana Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa da INEC ta yi.
Asali: Legit.ng