Gwamnan Gombe Ya Rushe Majalisar Zartaswa, Ya Ba Su Wa'adin Barin Ofis

Gwamnan Gombe Ya Rushe Majalisar Zartaswa, Ya Ba Su Wa'adin Barin Ofis

  • Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya sallami dukkan mambobin majalisar zartaswan gwamnatinsa
  • A wata sanarwa daga Ofishin sakataren gwamnatin, Yahaya ya ɗauki wannan matakin ne saboda karewar wa'adin zangon farko
  • Ya umarci duk wanda matakin ya shafa ya miƙa ragamar ma'aikata, ɓangare ko hukumar da yake jagoranta ga Sakatarensa

Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya rushe majalisar kwamishinoni da hadimansa, kuma ya roki dukkan waɗanda abun ya shafa su shirya barin Ofis.

Punch ta tattaro cewa gwamna Yahaya ya umarci dukkan naɗe-naɗen mambobin majalisar su rubuta takardar miƙa ragamar ma'aikatar da suke jagoranta gabanin ranar Laraba 19 ga watan Afrilu, 2023.

Gwamna Inuwa Yahaya.
Gwamnan Gombe Ya Rushe Majalisar Zartaswa, Ya Ba Su Wa'adin Barin Ofis Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Source: UGC

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 11 ga watan Afrilu, 2023, kuma an mata take da, "Miƙa ragamar ma'aikatu, sashi-sashi da hukumomi."

Kara karanta wannan

Shin An Biya Kuɗin Fansa? Ɗalibai Mata Na Jami'ar Tarayya Gusau Sun Kubuta Daga Hannun Yan Bindiga

Sanarwan na ɗauke da sa hannun Rabiu Abubakar, a madadin ofishin Sakataren gwamnatin jihar Gombe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubakar ya bukaci dukkan mambobin majalisar zartaswa da wannan mataki ya shafa su miƙa ragamar wurin da suke shugabanta hannun babban sakataren da ya dace da ma'aikatunsu.

Meyasa gwamna ya ɗauki wannan matakin?

Ya bayyana cewa gwamna Yahaya ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon nasarar da ya samu a a zaben gwamnan da aka kammala, wanda ya kawo karshen zangon mulkinsa na farko.

Sanarwan ta ce:

"Biyo bayan kammala zaɓen gwamnan 2023 wanda ya kawo karshen zangon farko na mulkin gwamna Muhammad Inuwa Yahaya (Ɗan Majen Gombe). An umarci na bukaci ku shirya bayanan miƙa ma'aikata, ɓangare da hukumomi."
"Bayanan da zaku rubuta ya ƙunshi duk wasu ayyuka da tsare-tsaren gwamnati da ba'a kammala ba. Muna bukatar ku miƙa bayanan Ofishin Sakataren gwamnati kafin ko ranar Laraba 19 ga watan Afrilu, 2023."

A wani labarin kuma Wani Gwamna Ya Dira Yola, Ya Yi Kus-Kus da Fintiri Kan Ayyana Binani a Matsayin Gwamnan Adamawa

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya Kan Babban Abu 1

Gwamnan jihar Oyo ya ziyarci takwaransa na jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri a gidan gwamnatinsa da ke Yola, babban birnin jihar.

Bayan ganawar gwamnonin 2, Seyi Makinde, ya yaba da namijin kokarin INEC a jihar Oyo, amma ya bukaci ta gaggauta gyara kuskurenta a jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262