Mai Shekara 32 a Duniya Ya Doke ‘Dan Siyasar da Ya Shafe Shekara 16 Yana Majalisa
- Bashir Usman Gorau aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaben ‘dan majalisar Gada da Goronya
- Hon. Musa S Adar ba zai koma Majalisar tarayya ba, bayan nasarorinsa a 2007, 2011, 2015 da 2019
- Kafin nasarar zababben ‘dan Majalisar, yana cikin Kwamishinoni a Gwamnatin Aminu Tambuwal
Sokoto - Bashir Usman Gorau ya yi nasara a kan Musa S Adar a zaben majalisar wakilan tarayya da hukumar INEC ta karasa a karshen makon jiya.
Daily Trust ta kawo rahoto cewa Honarabul Musa S Adar ya rasa kujerarsa ta ‘dan majalisar mai wakiltar Gada da Goronya a hannun jam’iyyar PDP.
‘Dan takaran na PDP da ya doke Musa S Adar a zaben bana shi ne Kwamred Bashir Usman Gorau.
Kafin zamansa ‘dan takarar majalisa, Bashir Gorau mai shekara 33 da haihuwa shi ne tsohon Kwamishinan harkokin matasa da wasanni na Sokoto.
A karshe PDP ta karbe Gada/Goranyo
Rahoton ya ce Hukumar INEC ta tabbatar da Kwamred Gorau ya samu kuri’u 29, 679 a zaben, sai ‘dan majalisa mai-ci ya zo na biyu da kuri’u 25,549.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon zaben da aka kammala ya tabbatar da cewa zaman Honarabul Adar ya zo karshe a majalisa, bayan ya shafe shekaru 16 yana wakilci.
Da a ce jam’iyyar APC ta yi nasara, za a rantsar da Adar a matsayin ‘dan majalisar Gada da Goronya a karo na biyar, ma’ana zai yi shekaru 20 a ofis.
The Cable ta ce tun bayan zaben 2007 ne Honarabul Adar ya tafi majalisa, a zabukan da aka shirya a 2011, 2015 da kuma 2019, duk shi ya samu nasara.
Mulki yana hannun Allah SWT
Da yake magana a shafinsa na Facebook a yammacin Lahadin da ta wuce, matashin ya godewa Allah SWT a kan wannan gagarumar nasara da ya samu.
Gorau ya jawo aya daga cikin Suratul Ali-Imran a Al-Kur’ani, yana nuna Ubangiji ne yake bada mulki ga wanda ya so, a lokacin da ya so, ga wanda ya so.
Wannan nasara ta na nufin an kara samun yawan matasan da za a rantsar a matsayin ‘yan majalisar tarayya, akwai sa’an Gorau da ya ci zabe a Kebbi.
"Gorau mutumin kirki ne"
Abubakar Umar Shattima wanda suka yi gwagwarmaya tare da zababben ‘dan majalisar a baya ya bayyana Bashir Gorau a matsayin jajirtaccen mutumi.
Shattima yake cewa ya san Gorau a matsayin mai kirki da taimakon matasa, musamman da ya rike kujerar Mai ba Gwamna shawara da Kwamishina.
A cewarsa, nasararsa a zaben darasi ce ga matasa, ya ce har abokan hamayyarsa su na murna.
Cin hanci a zaben Majalisa
Wasikar da Gwamnonin APC suka rubutawa Bola Tinubu ta nuna dole a dauki mataki a Majalisa, an ji labari ana jita-jita ana sayen kuri’un ‘yan majalisa.
Zargin da ake yi shi ne masu takara a majalisa sun shirya batar da $500, 000-$1m a kan kowace kuri’ar ‘dan majalisa da Sanata domin su lashe zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng