‘Dan Takaran da Ya Ki Biyan ‘Yan Jam’iyya ‘Ko Sisi', Ya Fado ta Kai a Neman Gwamna

‘Dan Takaran da Ya Ki Biyan ‘Yan Jam’iyya ‘Ko Sisi', Ya Fado ta Kai a Neman Gwamna

  • Sam Amadi yana cikin wadanda su ka nemi samun takarar Gwamnan jihar Imo a jam’iyyar LP
  • Tsohon shugaban na NERC bai yi nasara a zaben tsaida gwani da aka shirya a garin Owerri ba
  • Kafin a shiga zaben fitar da ‘dan takara, Amadi ya tabbatar da ba zai saye kuri'u da kudinsa ba

Imo - Sam Amadi wanda ya taba rike shugabancin hukumar NERC mai kula da harkar wuta a Najeriya, ya nemi tikitin Gwamna a jam’iyyar LP.

The Cable ta ce Sam Amadi ya shiga zaben fitar da gwani domin jam’iyyar hamayya ta LP ta tsaida shi a matsayin ‘dan takararta na Gwamnan jihar Imo.

A wani jawabi da ya fitar, Amadi ya ce ya shiga takarar kujerar Gwamna ne saboda jagorancin ‘dan takarar LP a zaben shugaban kasa, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Binani da Fintiri: Masanin siyasa ya yi hasashe, ya fadi wanda zai iya lashe zaben Adamawa

A cewarsa, yanzu ne lokacin da ya fi dacewa mutanen jihar Imo su zabi mutane masu gaskiya wadanda za su kawo karshen mulkin rashin gaskiya.

Tasirin Peter Obi a siyasar yau

"Nayi imani cewa jam’iyyar a karkashin jagorancin Peter Obi ta ba mutanen Imo dama domin su yi waje da shugabancin rashin gaskiya da ya yi kaka-gida.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Fitowar Peter Obi a matsayin haske mai maganin duhun siyasar Najeriya ya ba ni kwarin gwiwar cewa LP da yake jagoranta ta kawo sabon salon siyasa.

- Sam Amadi

‘Dan Takaran LP
Masoyan Peter Obi a Abuja Hoto: www.arise.tv
Asali: UGC

LP dabam da ragowar jam'iyyu

Rahoton ya ce Amadi ya nuna jam’iyyarsu ta LP ta sha bam-bam da sauran jam’iyyu da ake da su.

Bayan zama da ya yi da Obi da shugabannin jam’iyya na kasa, ‘dan takarar ya ce ya gamsu, zai nemi a tsaida shi ya rikewa LP tuta a zaben jihar Imo.

Kara karanta wannan

“Babu Wanda Zai Iya Tilasta Mani Barin Najeriya”, Peter Obi Ya Magantu Kan Tsare Shi Da Aka Yi a Ingila

Bayan ya yabawa ‘yan Obi-dients tare da jan kunne a kan irin abin da ya faru da jam’iyyar APGA, Amadi ya ce ba zai kashe kudi wajen samun tuta ba.

"Dole in fada da babbar murya ba zan biyewa masu saye da saida masu tsaida ‘dan takara ba. Na gabatar da kai na, kima, da jajircewa ta wajen kifar da Hope Uzodinma.
Masu tsaida ‘dan takara su zabe ni idan sun gamsu da sako na; ko su zabi wani idan su na son kudinsa."

- Sam Amadi

Achonu ya doke Sam Amadi

Ana haka sai ga rahoto cewa Sanata Athan Achonu ne ya lashe zaben da aka yi a jiya.

Calistus Ihejiagwa ya sanar da cewa Athan Achonu ya samu kuri’u 134, yana mai doke Janar Jack Ogunewe (mai ritaya), wanda ya zo na biyu da kuri’u 121.

APC ta rasa kujera a Kano

A wani rahoton, an ji yadda ‘Dan takaran Jam’iyyar NNPP ya hana LP ta karbe kujerar majalisar wakilan tarayya na bangaren Fagge da ke jihar Kano.

Kara karanta wannan

Zababben ‘Dan Majalisar Kano a Jam’iyyar NNPP Ya Rasa Kujerarsa a Gwamnatin Buhari

‘Dan takaran APC ya zo na uku ne a zaben, Aminu Goro wanda ‘Dan majalisa mai-ci ne ya rasa kujerarsa a hannun Barista Muhammad Bello Shehu na NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng